Bayyanar Ado Aleru Zaman Sasanci a Danmusa Ya Janyo Ce-ce-ku-ce a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes14062025_164309_FB_IMG_1749918169460.jpg

Katsina TIMES 

A wani mataki da ke kara tayar da kura a kokarin shawo kan matsalar tsaro a jihar Katsina, wani zaman sasanci ya gudana a karamar hukumar Danmusa, inda aka ga shahararren shugaban 'yan bindiga, Ado Aleru, wanda hukumomin tsaro ke nema ruwa a jallo.

Rahotannin da majiyar tsaro ta Zagazola Makama ta tattara sun nuna cewa Ado Aleru ya halarci zaman ne tare da wasu daga cikin wadanda ake zargi da hannu a rikicin, inda ya yi jawabi ga wakilan al’umma da shugabanni na gargajiya, yana bayyana wasu matakai da za su tabbatar da zaman lafiya tsakanin Fulani makiyaya da sauran al’ummar yankin.

Bayyanar Aleru a matsayin jagoran sasanci ya zo a daidai lokacin da jami’an tsaro ke ci gaba da kokarin cafke shi da kuma rusa hanyoyin sadarwarsa da mayakansa, sakamakon hare-haren da ake zarginsa da hannu a yankunan Arewa maso Yammacin Najeriya.

Masana da jama’a sun bayyana damuwa kan yadda wanda hukumomin tsaro ke nema za a bar shi ya bayyana a fili ba tare da an dauki matakin kama shi ba, musamman ganin irin tasirin da ya yi a wasu hare-hare da suka yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi.

Wannan zaman sasanci ya bayyana ne a matsayin wani sabon yunƙuri na hada tattaunawa da aiki tare da jami’an tsaro domin kawo karshen rikice-rikicen da suka daɗe suna addabar yankin. A baya, irin wannan shirin sasanci ya samu nasara a kananan hukumomin Batsari da Jibiya, inda aka samu saukin hare-hare da karancin garkuwa da mutane, sakamakon yarjejeniyar da aka kulla tsakanin bangarorin biyu.

Sai dai masana tsaro na jaddada cewa, ko da yake tattaunawa na da amfani wajen warware rikici, dole ne a ci gaba da daukar tsauraran matakan doka da oda domin tabbatar da cewa ba a mayar da zaman sasanci mafaka ga wadanda ke aikata laifuka ba.

Yayin da gwamnatin jihar Katsina ke kokarin ganin ta dakile 'yan ta'addan ta sabbin hanyoyi hadin gwiwa da jami'an tsaro don maido da doka da oda.

Follow Us