@ Katsina times
Gwamnatin Katsina ta kafa wani kwamitin da zai binciki yadda makarantun lafiya suke gudanar da ayyukan su. Kwamitin ya gano abubuwa masu ban tsaro a kan wasu makarantun.
Daga cikin abubuwan da aka gano akwai yadda wasu makarantun suka mayar da ba da takardun kammala su kamar wani kasuwanci.
Lamari mai hatsarin gaske ne ga lafiyar al'ummar jihar Katsina da arewacin Nijeriya.
Kwamitin ya yi aikinsa tsakani da Allah, inda ya rufe wasu makarantun, ya kuma nemi wasu makarantun su gyara kurakurensu kafin a buɗe su.
Wannan aiki da gwamnatin Katsina ta yi ya jawo mata addu'a, jinjina da yabo a duk faɗin jihar Katsina da maƙwabtanta. Saboda aiki ne na tseratar da rai da hana yaɗuwar annoba a jihar ta Katsina da maƙwabtanta.
Abin takaici, maimakon makarantun da aka ce su gyara kurakurensu, su mayar da hankalinsu wajen gyaran da neman su kai matsayin da za a iya buɗe su, amma sai ana zargin wasu suna neman mai da abin siyasa, inda suke ɗaukar nauyi ana zuwa a shafukan sada zumunta ana kiraye-kirayen wai Gwamna ya buɗe makarantun!
Ya buɗe makarantun kamar ya? Ba tare da sun cika ƙa'idar da aka ce kowa ya gyara ba? Shi ke nan sai ai ta samar da malaman lafiya na bogi su yi ta kisa da ɓarna a jihar Katsina?
Wasu makarantun da aka rufe a bayyane take suna ta ƙoƙarin gyara da cika ƙa'ida don su samu a buɗe su, su ci gaba da ayyukansu.
Binciken Katsina Times ya gano makarantu da yawa na ƙoƙarin cika cancanta. Misali a cikin Katsina makarantu irin su COGNET suna ta ƙoƙarin su ga sun cika ƙa'ida. A wajen Katsina, akwai makaranta irin su ALLIANCE da ke Dutsinma, duk suna wannan ƙoƙarin.
Amma ana zargin wasu, suna ƙoƙarin amfani da salon siyasa don tilasta wa gwamnati ta buɗe duk makarantun ba tare da cika ƙa'idojin da ya dace ba.
Mu a jaridun Katsina Times, muna ba duk makarantun da aka bai wa ƙa'idojin da za su cika shawarar su cika ƙa'idojin, sannan su nemi a buɗe su. Wannan shi ne zai tabbatar da suna kishin lafiyar al'ummar jihar Katsina, ba suna fifita samun kuɗi sama da kishin al'ummarsu ba.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar Taskar labarai
@ www.taskarlabarai.com
The links news
Facebook page Katsina city news
07043777779 08057777762.