@ Katsina times
Shugaban hukumar yaki da cutar kanjamau (HIV) na jahar Katsina, Dakta Nuhu Bala kankia ya bayyana ma jaridun Katsina times cewa, a katsina yaki da yaduwar cutar yana samun nasara sosai, kuma anyi nasara wajen dakile yaduwar ba kamar daba da take tafiya kamar wutar daji.
Shugaban ya kara da cewa, wannan nasara na tattare da goyon baya da suke samu daga gwamnatin Malam Dikko umar Radda PhD,wanda ya damu sosai da kula da lafiyar al ummar jahar Katsina.
Dakta ya kara da cewa tun a shekarar 2014 hukumar ta bar samun duk wani tallafi daga bankin duniya na tafiyar da ayyukan ta..sai ta koma gwamnatin jahar ke kula da gudanarwar hukumar.
Dakta Nuhu kankia ya kara da cewa,tun a shekarar 2018 aka tabbatar da jahar Katsina na da masu cutar ta kanjamau masu amsar magani a wajen hukumar su dubu 30,amma aikin hukumar na fadakarwa da wayar da kan jama a, ba dare ba rana ya sanya maimakon yawan ya karu raguwa yake.
Dakta Bala kankia ya kara da cewa, duk wani aikin kula da masu cutar Sida kyauta ne tun daga gwajin har zuwa bada magani.
Dakta Nuhu,ya jinjina ma gwamnan na katsina, ya kara da cewa yanzu haka gwamnatin ta katsina tana shirin sawo naurar nan wadda ake gwajin masu cutar da ita, wadda yanzu haka gwaje gwaje sai anje Kano.
Cikakkiyar hirar na nan tafe a shafukan Katsina times