Daga Muhammad Ali Hafizy | Katsina Times
Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta sake jaddada kudurinta na tabbatar da tsaftar harkokin gidajen otal a fadin jihar, tare da tabbatar da cewa masu gudanar da su suna bin doka da tsarin tarbiyya.
Shugaban hukumar, Dakta Aminu Usman Abu Ammar, ne ya jagoranci tawagar jami’an hukumar a ziyarar da suka kai gidajen otal da ke cikin birnin Katsina a ranar Alhamis, 10 ga watan Yuli, 2025.
A yayin ziyarar, Dakta Abu Ammar ya yi kira ga masu gidajen otal da su tabbatar da tsaftace harkokinsu, yana mai cewa kasancewar suna cin gajiyar harkokin kasuwanci daga wadannan gidaje, wajibi ne su tabbatar da cewa ana tafiyar da su ba tare da aikata alfasha ba.
"Mun lura da wasu ayyuka marasa kyau da ake aikatawa a wasu gidajen otal, musamman yadda ake bai wa mutane dakuna ba tare da tantance su ko bin ka'idoji ba," in ji shi.
Ya bayyana cewa rashin bin ka’ida wajen bayar da daki ga baƙi babban haɗari ne ga tsaro. "Idan wani abu ya faru, ba za a iya gano wanda ya sabawa doka ba saboda babu wata shaida da za ta nuna ko wanene shi. Daga yanzu, muna bukatar ku tabbatar da karbar wata takarda ko shaida daga kowane bako kafin a ba shi daki," in ji Dakta Abu Ammar.
Bugu da ƙari, ya gargadi masu gidajen otal da su guji bayar da dakuna ga mata masu zaman kansu da ake zargi da aikata alfasha da kuma yara ƙanana. Ya kuma umarce su da su rika taka-tsantsan wajen hana aikata alfasha a cikin otal-otal dinsu.
A ƙarshe, ya bukaci kada a rika ba wa 'yan garin Katsina hayar daki ba tare da wani kwakkwaran dalili ko hujjar da ta gasar ba.
Gidajen otal da hukumar ta ziyarta sun haɗa da: Alhayat, Faeez, Kaita Guest Inn, Murjani, Jamvalley, Green View, Katsina Tourist Lodge, Hill Side, King Paradise, Samari African Hotel, Hayatt, Zumunta, Gomad da Jakada Holiday.
Hukumar Hisbah ta bayyana cewa za ta ci gaba da irin waɗannan ziyarce-ziyarce don tabbatar da cewa gidajen otal a fadin jihar suna bin doka da kiyaye tarbiyya.