Daga Auwal Isah Musa | Katsina Times
Ma’aikatar Ilimi ta Firamare da Sakandare ta Jihar Katsina ta gudanar da bikin kaddamar da sabbin mambobin hukumar gudanarwa ta Hukumar Ilimin Manya ta Jihar Katsina. Taron rantsarwar ya gudana ne a ranar Juma’a, 11 ga Yuli 2025, a dakin taro na ma’aikatar da ke Katsina.
Kwamishiniyar Ilimi ta Firamare da Sakandare, Hajiya Zainab Musan Musawa, ce ta jagoranci Kaddamarwar inda ta taya sabbin mambobin murna tare da yabawa Gwamna Malam Dikko Umar Radda bisa himmarsa wajen inganta harkar ilimi a jihar.
Hajiya Musawa ta bayyana cewa zabin mambobin ya ta’allaka ne bisa cancanta, ƙwarewa da tarihin shugabanci da ayyukan jama’a. Ta bukace su da su yi aiki tare da kishin kasa domin gyara hukumar da kuma bunƙasa ilimin manya da na waje a fadin jihar.
“Nadinku alamar girmamawa ne bisa sadaukarwar ku ga ci gaban ilimi. Ana sa ran zaku shigo da ƙwarewarku da gaskiya domin jagorantar sabbin sauye-sauye masu amfani,” in ji kwamishiniyar.
A jawabinta na godiya, Daraktan Hukumar Ilimin Manyan Jihar Katsina Hajiya Bilkisu Muhammad Kaikai ta nuna godiya ga Gwamna Radda bisa hangen nesansa da goyon bayan da yake baiwa fannin ilimi. Ta kuma yaba da jajircewar kwamishiniya, tana mai bayyana taron a matsayin wata sabuwar dama ta ƙarfafa ayyukan ilimin manya.
“Ina taya sabbin mambobin hukumar murna da fatan alheri. Wannan kira ne na hidima,” in ji daraktan. “Ina roƙon Allah ya ba ku basira da amana wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanku. Ku sani kuna da goyon bayan cikakken na hukumar da kuma ma’aikatanta.”
Sabuwar hukumar na da rawar gani da ake sa ran za ta taka wajen tsara manufofi da tabbatar da ingantaccen tsarin ilimi ga manya da wadanda ba su samu damar shiga makaranta ba a jihar.
An naɗa Dr. Aisha Ladan a matsayin shugabar hukumar, yayin da sauran mambobin da aka rantsar su ne: Adamu Sule (Jibia), Nazifi Abdulkadir (Batagarawa), Hajiya Saratu Ibrahim (Danja), da kuma Sani Maibara (Baure).
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati ciki har da Babbar Sakatariya ta Ma’aikatar, Hajiya Ummul-Khairi Bawa, da Sakataren Hukumar Ilimin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Katsina, Farfesa Kabir Ibrahim Matazu, da sauran manyan baki.