Ƙungiyar Raya Wasanni da Al’adun Gargajiya ta Jihar Katsina ta kai ziyarar ban girma ga Hukumar Kula da Tsaro da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Jihar Katsina (KASSAROTA), domin neman haɗin gwiwa a kan shirin wayar da kai game da tsaron hanya da bin doka da oda a titunan jihar.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na KASSAROTA, Marwana Abubakar Kofar Sauri, ya fitar ga manema labarai.
A yayin ziyarar, shugaban ƙungiyar, Malam Musa Wakili, ya bayyana cewa haɗin gwiwar ƙungiyar da KASSAROTA zai taimaka wajen sauƙaƙa isar da saƙon wayar da kai ga al’umma, musamman ta hanyar amfani da wasan kwaikwayo da al’adu wajen isar da saƙonni masu muhimmanci kan dokokin hanya.
Ya ce: “KASSAROTA tana taka muhimmiyar rawa wajen kare rayuka da dukiyoyi a fadin jihar Katsina. Muna ganin dacewar mu hada kai da su domin faɗakarwa ga jama’a, musamman a yankunan karkara.”
A nasa jawabin, Darakta Janar na KASSAROTA, Manjo Yahaya Garba Rimi (rtd), ya bayyana farin cikinsa da ziyarar, yana mai cewa ƙawancen ya yi daidai da hangen nesa na Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D., CON, wanda ya bai wa batun tsaron hanya muhimmanci a gwamnatinsa.
Manjo Rimi ya bayyana cewa yawaitar haɗurran hanya a jihar na barazana ga lafiyar jama’a da tsaron su, yana mai zargin rashin bin ƙa’idojin zirga-zirga a matsayin babban abin da ke haddasa su. Ya jaddada damuwarsa kan yadda direbobi ke cunkushe motocin haya da fasinjoji sama da ƙima — inda motar da aka tsara don fasinjoji biyar ke ɗaukar har goma ko sama da haka, wanda ke haddasa haɗura.
Ya yaba wa shugabannin ƙungiyar bisa ƙoƙarinsu na amfani da fasahar wasan kwaikwayo da al’adu wajen goyon bayan aikin KASSAROTA na wayar da kai da tabbatar da bin doka a tituna.
Darakta Rimi ya tabbatar da cewa hukumar KASSAROTA a shirye take ta yi aiki tare da kowane bangare a fadin jihar domin cimma burinta na kare rayuka da dukiyoyi, da kuma samar da tsaro a hanyoyin jihar Katsina.