Kwalejin Lafiya Ta Khuddam A Katsina Ta Yi Babban Taron Bikin Yaye Dalibai

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes25072025_205650_FB_IMG_1753476865641.jpg

.

Kwalejin Ilimin lafiya ta 'Khuddan College Of Health Science And Technology Katsina' ta gudanar da babban taron bikin yaye daliban makarantar karo na biyu.

Bikin yaye daliban ya gudana ne a dakin taro na Makarantar da ke kofar Kaura a ranar Juma'ar nan, inda ya samu halartar Malamai, Iyayen dalibai, dangi da abokan daliban da aka yaye.

Da yake tsokaci a matsayinsa na babban bako a bikin, Malami daga kwalejin kimiyya da fasaha ta Hassan Usman Katsina Polytechnic, Dr. Bashir Usman Ruwan Godiya, ya hori daliban da su yi aiki da abin da suka karanta, musamman da karatun nasu ya kasance na ceton rayukan al'umma ne kaitsaye.

Ruwan Godiya, ya kuma gargade su cewar, ahir din su da sabawa ka'ida da dokar Ilimin nasu ta kowace fuska, yana mai kwatanta hakan da abin da zai iya jawo nakasa ko makancin haka ga majinyaci (Allah ya kiyaye).

Shugaban makarantar, Dr. Kabir Muhammadu Sa'id, a taron, ya ce adadin daliban da suka suka kammala makarantar a wannan karon su 119 ne wadanda suka fito daga mabambanta tsangayoyi (departments) na makarantar, yana mai shaidarsu da samun nagartaccen karatu da kuma kwarewa kan abin da suka karanta.

A wajen bikin, faukacin daliban da aka yaye sun karbi rantsuwar tabbatarwa a matsayin jami'an lafiya, bisa alkawalin yin aiki a kan doron dokar da harkar lafiya ta tanadar don ceton rayukan al'umma da inganta lafiyar al'umma, inda aka ba kowanensu ahaidar kammala karatunsa (Certificate).

Bugu da kari, duk a wajen bikin yayen, an kuma karrama wasu Malaman makarantar da lambar girmamawa sakamakon jajircewarsu ga daliban, kazalika an kuma ba wa wata daliba daga cikin daliban da suka kammala, Sakina Hassa, shaidar yabo a matsayin ta "Gwarzuwar Shekara" saboda irin hazakarta a makarantar.

Follow Us