Daga Wakilinmu | KatsinaTimes
A ranar Litinin, 28 ga Yuni, 2025, Gidauniyar Yakubu Ali Mai Canji, ƙarƙashin jagorancin Yakubu Ali Mai Canji, ta raba tallafin kuɗi da ya kai Naira miliyan uku ga mata 150 daga Mazabar Arewa “A” da ke cikin birnin Katsina.
An gudanar da bikin rabon tallafin ne a harabar makarantar firamare da ke cikin rukunin gidajen gyaran hali a unguwar Yari, inda aka samu halartar wakilai daga majalisar dokokin jihar Katsina, shugaban karamar hukumar Katsina, Malam Isah Miqdad, da sauran dattawa da masu ruwa da tsaki a yankin.
A jawabin daya daga cikin masu shirya wannan shiri, Sani Arqb, ya bayyana cewa kowace mace ta samu Naira dubu 20 domin ta fara ƙaramin kasuwanci a gida. Ya ce: “Mun bi rumfuna 19 da ke cikin mazabar, inda muka zabi mace uku daga kowace rumfa, sannan muka ƙara da wasu daga cikin magoya bayanmu. Amma mun kuma zaɓi mata daga kowace jam’iyya da muka tabbatar suna cikin buƙata domin su ma su ci gajiyar shirin.”
Dan majalisar dokokin jihar Katsina, Hon. Aliyu Abubakar Albaba, ya bukaci matan da suka amfana da su yi amfani da kuɗin wajen inganta rayuwarsu ta hanyar da ta dace.
Shi ma a nasa jawabin, shugaban karamar hukumar Katsina, Malam Isah Miqdad, ya jinjinawa Yakubu Ali Mai Canji bisa ƙoƙarinsa da kishinsa ga al'umma. Ya ce, “Da ace a kowace mazaba akwai matashi kamar Yakubu Mai Canji, da tuni an rage matsalar rashin aikin yi a Katsina.”
Miqdad ya yi kira ga masu hannu da shuni da su rika tallafawa marasa ƙarfi ta hanyar samar da jarin kasuwanci musamman ga Mata, domin taimakawa gwamnati rage matsalolin da jama’a ke fuskanta. Ya rufe jawabin nasa da addu’ar fatan alheri tare da gudanar da rabon tallafi ga wasu mata uku a fili, yayin da sauran manyan baki suka ci gaba da raba tallafin ga sauran mata da suka samu.