Daga Katsina Times | 30 Yuli, 2025
Babbar Kotun Jihar Katsina mai lamba 9, karkashin jagorancin Mai Shari’a I.I. Mashi, ta yanke hukuncin kisa ga mutum biyu da aka samu da laifi a kisan gilla da aka yi wa tsohon Kwamishinan Kimiyya da Fasaha na Katsina, marigayi Honourable Rabe Nasir, a shekarar 2021.
Kotun ta tabbatar da cewa Shamsu Lawal tsohon mai gadin marigayin da Tasi’u Rabi’u wanda ke aikin girki a gidan mamacin sun bai wa Rabe Nasir abinci mai guba wanda ya kashe masa jiki don ya gaza komai sai yanda akai da shi, wanda ya janyo mutuwarsa, bayan an samu damar caccaka masa wuƙa. Hakan ya tabbata ne bisa binciken da asibiti ta gudanar, wanda ya nuna akwai guba a jikin mamacin, da kuma hujjojin binciken 'yan sanda.
Baya ga hukuncin kisa da aka yanke wa mutum biyun, kotun ta kuma yanke hukuncin dauri na shekaru biyar a gidan yari ga wani tsohon mai gadi, Sani Sa’adu, bayan da aka same shi da laifin boye gaskiya game da lamarin kisan.
A gefe guda, kotun ta sallami wata yarinya mai suna Gift Bako, wadda aka kasa gabatar da hujjoji masu gamsarwa da ke da nasaba da laifin. Lauyanta, Barista Shedrack, ya yaba da hukuncin kotun, yana mai cewa hukuncin ya tsaya kan gaskiya. Haka kuma, lauyoyin dukkan ɓangarorin sun bayyana gamsuwarsu da yadda shari'ar ta gudana da kuma hukuncin da aka yanke.
Lauyan waɗanda aka samu da laifi, Barista Ahmad Murtala Kankia, ya roƙi kotu da ta yi sassauci a hukuncin, yana mai jaddada cewa wadanda lamarin ya shafa na da nauyin iyaye da iyali da ke dogara da su. Sai dai, lauyar masu gabatar da kara, ta nuna jin daɗinta da hukuncin, inda ta ce ya yi daidai da doka kuma an samu adalci.
Wakilan Katsina Times da suka halarci zaman kotun sun shaida cewa wadanda aka yankewa hukuncin sun shiga cikin firgici lokacin da jami’an tsaro suka shigar da su cikin mota domin wucewa da su gidan yari. Haka zalika, an hangi farin ciki da jin daɗi a fuskar ‘yan uwa da lauyoyin Gift Bako bayan kotun ta wanke ta daga zargin.
Marigayi Rabe Nasir ya rike mukamin Kwamishinan Kimiyya da Fasaha a Jihar Katsina a lokacin gwamnatin tsohon Gwamna Aminu Bello Masari. Haka kuma, ya kasance ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Mani da Bindawa a shekarar 2003, tare da riƙe mukamin jami’in hukumar DSS a baya.
A bangare guda, akwai wasu mutane biyu da ke da hannu a shari’ar, da suka kai kara a Babbar Kotun Kaduna, suna neman dakatar da cigaban shari’ar a Katsina.
Katsina Times za ta kawo maku rahoto na musamman a kan batun.