Mu’azu Hassan | Katsina Times
Ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar APC a Jihar Katsina da ƙasar baki ɗaya, Sanata Abubakar Sadiq 'Yar'adua, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.
Sanata Sadiq, ƙwararren ɗan jarida ne kuma gogaggen ɗan siyasa, wanda ya fara samun nasara a harkar siyasa tun daga shekarar 1999, inda ya wakilci karamar hukumar Katsina a Majalisar Wakilai har zuwa 2003. Daga nan kuma, ya zama Sanata mai wakiltar yankin Katsina ta Tsakiya daga shekarar 2011 zuwa 2015.
Tun daga jam’iyyar ANPP zuwa APC, Sanata Sadiq na daga cikin jagororin da suka riƙa jagorantar jam’iyyun adawa har suka kafa gwamnati a matakin tarayya. A siyasance, ana kallon sa a matsayin ɗaya daga cikin fitattun ’yan siyasan da suka gina matasa da sabbin ’yan siyasa a yankin Katsina ta Tsakiya.
A wani lokaci, ya kasance mai taimaka wa Hon. Aminu Bello Masari lokacin da yake Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya.
Sanata Sadiq ya kammala digirinsa na farko a fannin aikin jarida. Daga nan ya samu digiri na biyu a fannin kimiyyar siyasa, da kuma wani digiri a harkokin hulɗar ƙasa da ƙasa. Yana da digirin digirgir (Ph.D.) a fannin lauya.
A matakin aiki, ya riƙe mukamai daban-daban a hukumomin gwamnatin tarayya da kuma a Jihar Katsina. Yana da tarihin aiki a sassa daban-daban na gwamnati da suka shafi cigaban jama’a.
Har wa yau, yana daga cikin marubutan da suka ba da gudunmawa wajen rubuce-rubuce na tarihi, inda ya rubuta tarihin tsohon gwamnan Katsina, Kanal Yahaya John Madaki.