Sabuwar Dokar Masarautu Ta Katsina: Ga Abin Da Ta Ƙunsa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes05082025_011458_FB_IMG_1754355040550.jpg

Sabuwar Dokar Masarautu Ta Katsina: Ga Abin Da Ta Ƙunsa

Muazu Hassan | Katsina Times

Majalisar dokoki ta jihar Katsina ta kammala karatu na uku tare da amincewa da sabuwar dokar masarautu a makon da ya gabata.

Doka ce da yanzu ake jiran Gwamna Dikko Umar Radda ya sanya wa hannu, sannan a fitar da ita a gazette domin ta zama cikakkiyar doka da za a fara amfani da ita a faɗin jihar Katsina.

A cewar binciken da Katsina Times ta gudanar, dokar na ɗauke da shafuka goma sha takwas (18), inda ta kunshi muhimman sauye-sauye da suka shafi tsarin gudanarwar masarautu a jihar.

Muhimman Sauye-Sauyen da Sabuwar Dokar Ta Ƙunsa:

1. Ƙirƙirar Majalisar Masarautu:
A karkashin sabuwar dokar, an kafa Majalisar Masarautu ta Jihar Katsina, wacce ta ƙunshi masarautun Katsina da Daura. Kowace masarauta za ta samu wakilci kamar haka:

Sarkin masarauta a matsayin Shugaban Majalisa (Chairman)

Masu sarauta shida (6)

Wakilai biyu daga malaman addini

Wakilai biyu daga 'yan kasuwa

Wakili ɗaya daga ƙungiyoyin matasa

Wakilin kwamishinan kananan hukumomi

Wakili daga Ma’aikatar da ke kula da masarautu

Masu zaɓen sarki

2. Ayyukan Majalisar:
Dokar ta fayyace ayyukan wannan Majalisa har guda goma (10) a kowace masarauta.

3. Matsayin Sarakuna:
Dokar ba ta bar wa gwamna ikon ƙayyade matsayin kowanne sarki ba – misali daga mai daraja ta ɗaya zuwa ta uku.

4. Zaɓen Masu Zaɓen Sarki:
Gwamna zai iya zaɓar ɗaya daga cikin masu zaɓen sarki, bisa amincewar rinjaye daga majalisar dokoki ta jihar Katsina.

5. Ayyukan Masu Zaɓen Sarki:
An fayyace aikinsu a masarautun Katsina da Daura, tare da sunayensu da yadda za a gudanar da nadin sarki ko sauke shi.

6. Sakataren Majalisa:
Hukumar kula da Ma’aikatar kananan hukumomi za ta naɗa sakatare a majalisar masarautu daga cikin ma’aikatan gwamnati. Dokar ta fayyace ayyukansa da yadda za a gudanar da su.

7. Gudanar da Kuɗin Masarautu:
Dokar ta bayyana yadda za a sarrafa kuɗin masarautu. Gwamna, bisa shawarwarin Hukumar da ke kula da Ma’aikatar Kananan Hukumomi, zai naɗa akawu da mai binciken kuɗi a kowace masarauta. Ayyukan su suma sun bayyana a cikin dokar.

8. Shugaban Majalisar Sarakuna:
Gwamna ne ke da ikon naɗa shugaban Majalisar Sarakunan Katsina, tsakanin Sarkin Katsina da Sarkin Daura.

9. Sakataren Majalisar Sarakuna:
Hakanan, Gwamna zai naɗa sakataren majalisar sarakuna na jihar, tare da fayyace aikinsa da na majalisar gaba ɗaya.

10. Rushe Tsohuwar Doka:
Sabuwar dokar ta rushe tsohuwar dokar masarautun da ake amfani da ita tun shekarar 1979.

Katsina Times
www.katsinatimes.com
07043777779

Follow Us