Wata kungiya mai rajin kare muradun almajirai da malamai daga tsangayoyin Alkur’ani mai suna Tsangaya Abar Alfaharinmu da ke karamar hukumar Nassarawa, Kano, ta aike da wata budaddiyar wasika zuwa ga Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, tana mai neman goyon bayan gwamnatinsa wajen inganta rayuwar almajirai da malaman tsangaya a fadin jihar.
A cikin wasikar da shugaban kungiyar, Sanin Malam Muhammad Sani Musa Nuhu ya rubuta, kungiyar ta bayyana irin gudummawar da suka bayar wajen tallafawa gwamnatoci a lokutan da suka gabata, musamman ta fuskar addu’o’i da wayar da kan al’umma wajen yakar zalunci da tabbatar da adalci, tun daga shekarar 2015 zuwa 2019.
“Mun taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa tafiyarku, ta hanyar addu’o’i, rubuce-rubuce da amfani da kafafen sada zumunta. Amma har yanzu ba mu ji a jikimmu daga romon demokraɗiyyar gwamnatinku ba,” in ji wasikar.
Kungiyar ta yi nuni da cewa duk da irin ayyukan alheri da gwamnan ke gudanarwa a fadin jihar, amma tsangayoyin Alkur’ani da almajirai ba su ji daɗin wannan ci gaba ba. Wasikar ta ce almajirai da malamai a Kano sun kai kusan tsangayoyi 13,000, amma har yanzu suna cikin matsanancin hali.
Wasikar ta lissafo wasu daga cikin muhimman bukatun da suka shafi tsangayoyin, kamar haka:
1. A ba almajirai wakilci a sabuwar Majalisar Koli ta Malaman Jihar Kano.
2. A samar da fitilun hasken lantarki (solar) a tsangayoyi domin sauƙaƙe karatu.
3. A ware musu kaso a kasafin kuɗin kowace shekara.
4. A gyara rumfunan karatu, dakunan kwana da bandakuna.
5. A gina rijiyoyin burtsatse a tsangayoyi domin samun tsaftataccen ruwan sha.
6. A rika karrama fitattun malamai da almajirai irin yadda ake yi wa malaman Islamiyya.
7. A samar da tsangayoyi na dindindin a fadin jihar.
8. A gudanar da zaman shawara da wakilan tsangayoyi kai tsaye.
9. A rika ware kaso a kowanne tallafi da gwamnati ke bayarwa.
10. A ɗauki almajirai a cikin shirye-shiryen koyon sana’o’i da bayar da tallafin jari.
11. A ba tsangayoyi kaso mai tsoka a rabon taki na zamani.
Kungiyar ta kuma yaba da nadin da Gwamna Abba ya yi wa daya daga cikin malaman tsangaya, Gwani Musa Falaki, a matsayin mai bai wa gwamna shawara kan harkokin tsangaya, da kuma tallafin da ake bai wa daliban da ke karatu kyauta a gidan jagoran jam’iyyar NNPP, Injiniya Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.
A ƙarshe, kungiyar ta jaddada cewa inganta tsangayoyi da rayuwar almajirai zai taimaka matuƙa wajen samun zaman lafiya, ci gaba da kuma ƙarfafa mulkin gwamnatinsa.
“Muna fatan Gwamna Abba zai ɗauki wannan kira da muhimmanci, domin ƙarin ɗaukaka gwamnatin sa da kawo ci gaba mai ɗorewa ga al’ummar Kano,” in ji Sanin Malam.
Wasikar dai ta ƙare da addu’o’i da fatan alheri ga jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya.