Barayin Intanet Sun Kwaikwayi Muryar Sakataren Gwamnatin Tarayya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes08082025_132954_senator-a.jpg

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya gargadi jama’a kan wani sabon salo na wasu ‘yan damfara da suka kwaikwayi muryarsa domin yaudarar manyan mutane da alkawarin ba su mukaman gwamnati.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Yomi Odunuga, ya fitar, Akume ya bayyana cewa, barayin sun yi amfani da fasaha wajen kwaikwayon muryarsa da kuma lambar wayarsa domin neman kuɗi daga wadanda suke cewa za a nada su a mukaman gwamnatin tarayya.

“Daga bayanan da muka samu, wadannan barayin sun kwaikwayi muryata da kuma lambobin waya, suna amfani da su wajen neman kuɗi daga wadanda suke yi wa alkawarin mukaman gwamnati,” in ji shi.

Ya kara da cewa, barayin suna amfani da dabarar sanar da wanda suka yi niyyar yaudarawa cewa sun riga sun saka sunansa a jerin wadanda za a nada a wani mukami, sannan su bukaci a tura musu kuɗi tsakanin naira miliyan biyar zuwa naira miliyan goma sha biyar, tare da aika musu da bayanan asusun banki da kuma bukatar a tura musu takardun neman aiki ta imel da suka kwaikwaya.

Ofishin sakataren ya ce ya sha samun korafe-korafe da tambayoyi daga jama’a kan wannan mummunan aika-aika, don haka ya zama wajibi a yi wannan gargadi ga jama’a su yi hattara da irin wannan makirci.

Odunuga ya bukaci jama’a su tabbatar da tantance sahihancin duk wata mu’amala kafin amincewa, tare da nisantar duk wani bukatar kuɗi da aka ce wai don samun mukaman gwamnati.

Follow Us