Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin gina sabon layin dogon jirgin kasa na haske a cikin birnin Kano da kudinsa ya kai Naira tiriliyan 1.5. Shugaban Kwamitin Kidaya Kudin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai, Hon. Abubakar Kabir Abubakar (Bichi) ne ya bayyana hakan a tattaunawarsa da manema labarai a Kano. Ya ce wannan aiki zai rage matsalolin sufuri a cikin birnin Kano, inda ya kara da cewa irin wannan aikin ana ganinsa a kasashen Turai da yankin Asiya, kuma yana da matukar amfani wajen bunkasa tattalin arzikin jihar bayan kammalawa.
Hon. Bichi ya musanta rade-radin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya sanya ayyuka a Arewa, inda ya bayyana cewa shugaban kasa ya kaddamar da muhimman ayyuka a fannoni daban-daban kamar su gine-gine, lafiya, noma, ilimi da tsaro a yankin. Ya ce daga cikin ayyukan akwai aikin hanyar Kaduna–Zaria–Kano wanda ya kusa kammaluwa, da aikin Kaduna–Abuja mai tsawon kilomita 400 da aka sake bai wa wani kamfani wanda yanzu aikin ya fara tafiya cikin sauri, tare da burin kammala shi kafin karshen zangon farko na shekara mai zuwa. Haka kuma, akwai aikin hanyar Kano–Hadejia mai tsawon kilomita 200 da aka kammala, da kuma hanyar Kano Northern Bypass da ta kai sama da Naira biliyan 250.
Ya bayyana cewa ziyararsu a Kano ta yi daidai da taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC domin tsara dabarun samun nasara a zaben 2027. Ya tunatar da cewa a zaben 2023, Kano ta bai wa Shugaba Tinubu kuri’u sama da 500,000 — mafi girma a duk fadin kasar. Haka kuma, taron ya kasance na nuna goyon baya ga tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya samu nasarar sauya jihohin PDP da dama zuwa hannun APC.