Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
Hukumar Kula da Mahajjatan Kiristoci ta Najeriya (NCPC) ta sanar da cewa za a ci gaba da gudanar da aikin ziyara zuwa ƙasashen Isra’ila da Jordan a watan Satumba mai zuwa, bayan dage takunkumin da aka sanya a baya saboda tashin hankali a Gabas ta Tsakiya.
Sakataren Zartarwa na hukumar, Bishop Stephen Adegbite, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta amince da tallafin kaso 50 cikin 100 na kuɗin tafiya, wanda hakan ya rage wa mahajjata kuɗin zuwa Naira miliyan 4.5 kacal.
A baya NCPC ta dakatar da shirin zuwa Isra’ila har sai an samu sulhu tsakanin Isra’ila da Iran. Sai dai a cewar Adegbite, yanzu an samu kwanciyar hankali da izinin ci gaba da tafiya.
“Na dawo daga Isra’ila a makon da ya gabata tare da wasu mambobin Majalisar Wakilai. Komai lafiya lau yake, babu wata matsala. Saboda haka za mu fara tafiyar daga ranar 14 ga Satumba, inda jirgin farko zai tashi daga jihar Imo,” in ji shi.
Adegbite ya bayyana cewa tafiyar za ta ɗauki kwanaki 10, kuma an tanadi tsare-tsare na musamman domin tabbatar da tsaron mahajjata da lafiyarsu, duk da yiwuwar sake samun matsalolin tsaro a yankin.
Haka kuma, ya ce hukumar ta shirya tafiyar “Executive Pilgrimage” tare da kusan mambobin Majalisar Wakilai 100 kafin babban aikin ziyarar Easter da za a kaddamar daga Imo ranar 14 ga Satumba, 2025.