Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa dalibai 8,971 daga jami’o’in tarayya a shiyyoyin Arewa maso Yamma sun ci gajiyar tallafin karatu na Nigerian Education Loan Fund (NELFUND) da aka kaddamar domin rage wa iyaye da ɗalibai nauyin kuɗin karatu. Ministan Yaɗa Labarai da wayar da kan al’umma, Alhaji Muhammad Idris, ne ya bayyana haka a Kano a yayin gabatar da rahoton rabin wa’adin mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Idris, wanda Daraktan Hukumar Wayar da Kai ta Kasa (NOA), Rabiu Ado ya wakilta, ya ce jami’ar Bayero Kano (BUK) ta fi kowacce jami’a yawan masu cin gajiyar shirin a fadin kasa. Ya bayyana cewa Jami’ar Tarayya Dutsinma ta samu Naira miliyan 409, Jami’ar Tarayya Dutse ta samu Naira Miliyan 593, yayin da Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato (UDUS) ta amfana da Naira Miliyan 578. Ministan ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta ɗaukaka Kwalejin Ilimi ta Kano zuwa Jami’ar Ilimi, tare da sauya kwalejin fasaha ta Kabo zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha.
Ya kuma bayyana cewa kafa Hukumar Cigaban Arewa maso Yamma (NWDC) mai hedikwata a Kano zai hanzarta ci gaban abubuwan more rayuwa da haɓakar tattalin arziki a yankin. Haka kuma ya ce ana gina gidaje 5,000 a dukkan jihohin shiyyar, sannan aikin hanyoyi da jiragen ƙasa kamar Kano–Katsina–Maradi line, Kano–Kaduna super highway da Sokoto–Tambuwal–Jega road na cigaba da tafiya domin sauƙaƙe sufuri da kasuwanci. A fannin makamashi kuwa, ya ce ayyukan wutar lantarki irin su Kano–Daura–Katsina wind project da Kano Power Project (KKMP) na gudana don inganta samar da wuta a shiyyar.