Mataimakiyar Shugaban Majalisar Matasan Najeriya (NYCN) reshen Jihar Katsina, Amb. Khadija Saulawa, ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da ta dauki matakan gaggawa wajen kubutar da mata 60 da aka ce an sace a harin ‘yan bindiga a karamar hukumar Malumfashi.
A cikin jawabin ta, Saulawa ta bayyana damuwarta kan yadda matsalar tsaro ke cigaba da barazana ga rayuwar jama’a, musamman a yankunan karkara, inda ta buƙaci gwamnati da hukumomin tsaro su dauki matakan da suka dace domin ganin an dawo da matan cikin koshin lafiya.
Sai dai, har yanzu hukumomin tsaro da na gwamnati ba su fitar da cikakken bayani kan wannan rahoto ba, ko kuma matakan da ake dauka don kubutar da waɗanda ake zargin an sace.
Rahotanni sun nuna cewa a baya-bayan nan an samu irin wadannan hare-hare a wasu sassan jihar, abin da ke kara tayar da hankulan jama’a da bukatar daukar matakan tsaro na musamman.