Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, 22 ga Agusta, 2025
Gwamnatin Jihar Katsina ta kaddamar da wani gagarumin shirin sauya tsarin ilimi ta karkashin Transforming Education System at State Level (TESS), wanda ya mayar da hankali kan amfani da fasahar zamani wajen koyarwa, inganta tsaro, da kuma kyautata jin dadin malamai da ɗalibai.
A cikin wata tattaunawa ta musamman da Katsina Times ta yi da ita a ranar Juma’a, Koodinetan shirin TESS ta Katsina, Hajiya Binta Abdulmumini Ahmed, ta bayyana cewa gwamnatin Gwamna Dikko Umaru Radda, tare da hadin gwiwar Bankin Duniya, ta kawo na’urorin zamani domin sauya tsarin koyarwa a ajujuwa na fadin jihar.
Hajiya Binta ta bayyana cewa wannan shiri zai kawar da tsohon tsarin koyarwa na gargajiya zuwa hanyar koyarwa ta dijital.
“Tsawon lokaci malamai da dama suna samun ƙalubale wajen shirya darussa, wasu ma kan shiga aji ba tare da cikakken shiri ko kuma bin manhajar kasa ba. Amma yanzu, an tanadar da kwamfutar hannu (tablet) da aka saka darussa na Ingilishi, Lissafi da Kimiyya, domin sauƙaƙa musu shiryawa da koyarwa,” in ji ta.
An samar da wadannan na’urorin tare da ƙaramin batirin ajiya (power bank) kuma suna aiki ba tare da dogaro da intanet ko wutar lantarki ba, domin amfanin makarantu da ke fama da matsalolin wuta.
Baya ga fasahar zamani, shirin ya kuma shafi tallafa wa ɗalibai da ba su da galihu da kayan makaranta kyauta. Haka kuma an girka kyamarar tsaro ta CCTV a makarantu 130 a dukkan kananan hukumomin jihar a matakin farko na shirin tsaro.
“Kyamarorin tsaro za su taimaka wajen kare dalibai, tabbatar da gaskiya da kuma inganta yanayin karatu mai aminci. Ana sa ran karin makarantu za su ci gajiyar wannan tsari a matakai na gaba,” in ji Hajiya Binta.
Domin tabbatar da tsaro da adalci wajen amfani da na’urorin koyarwa, an samar da tsarin kulawa. Kowace kwamfutar hannu na dauke da lambar gano mallaki, inda malamin da ya karɓa zai sanya hannu a kan yarjejeniyar amana.
“Muna da bayanan albashi da lambobin CE na kowanne malami. Idan aka rasa ko aka lalata na’ura saboda sakaci, za a iya gano ta kuma a cire kudin maye gurbin daga albashin malamin,” in ji ta.
A wani bangare na shirin, za a fara horas da malamai 10,000 kan yadda za su yi amfani da fasahar zamani, shirya darussa, da kuma amfani da na’urorin koyarwa a cikin aji daga ranar Litinin, 25 ga Agusta, 2025.
Hajiya Binta ta nanata cewa shirin TESS wata sabuwar nasara ce ga harkar ilimi a Katsina, domin yana nufin bai wa malamai da ɗalibai kayan aiki na zamani da za su basu damar dacewa da wannan sabon zamani, tare da ƙarfafa tsaro, ladabi da kuma gaskiya a makarantu.