Daga Katsina Times | Jumma’a, 22 ga Agusta, 2025
Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da aniyar ta na cafke da kuma gurfanar da masu hannu a harin da ya yi sanadin mutuwar wasu masallata a Ƙaramar Hukumar Malumfashi ta Jihar Katsina.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, wanda ya fitar da sanarwa a ranar Juma’a, ya bayyana wannan hari a matsayin “mugun aiki na rashin imani da ta’addanci”, tare da jaddada cewa ba zai wuce ba tare da hukunci ba.
Ya ce: “Jami’an tsaro suna kan bincike tare da bin sawun waɗanda suka aikata wannan danyen aiki. Ba za a bar wata kafa ba sai an kama su, kuma an hukunta su yadda ya dace.”
Ministan ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tabbatar wa da ‘yan ƙasa cewa adalci zai tabbata cikin gaggawa da ƙarfi, domin ba za a taɓa bari irin waɗannan ayyukan su zame ruwan dare a ƙasar nan ba.
Shugaba Tinubu ya miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasu, al’ummar Malumfashi da kuma Gwamnatin Jihar Katsina. Idris ya ce: “Damuwa da ɓacin ransu tamu ce, kuma gwamnati tana tare da su a wannan lokaci mai cike da ƙunci. Allah Maɗaukaki ya jiƙan mamatan, ya kuma ba iyalansu da al’umma ƙarfin zuciya da juriyar ɗaukar wannan babban rashi.”
Ministan ya kuma bayyana cewa nasarori masu muhimmanci suna ci gaba da samu a yaƙin da ake yi da ta’addanci, inda Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC) ta samu damar cafke manyan shugabannin ƙungiyoyin ta’addanci, ciki har da Mahmud al-Nigeri na ƙungiyar Mahmuda, mataimakinsa Abu Abba, da kuma Mahmud Muhammad Usman (Abu Bara’a) na ƙungiyar Ansaru – waɗanda dukkan su ke cikin jerin masu laifi da ake nema a duniya.
“Wannan nasara ta nuna sakamakon ƙoƙarin da ake yi a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Tinubu, wanda ya bayyana a fili cewa ayyukan ta’addanci da ke barazana ga ƙasar nan da ‘yan ƙasa ba da jimawa za su zama tarihi,” in ji Idris.
Ya jaddada cewa gwamnati ba za ta taɓa barin wanda ya zubar da jinin jama’a ya samu mafaka a Nijeriya ba.