Katsina Times
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Katsina (KTSIEC) ta sanar da fara gudanar da rajistar katin zabe a dukkan sassan jihar.
Shugaban hukumar, Alhaji Lawal Alhassan Faskari, ne ya bayyana hakan a yayin taron manema labarai da aka gudanar ranar Talata, 26 ga Augusta, 2025, wanda jaridun Katsina Times suka halarta.
A cewarsa, wannan aikin wani muhimmin aiki ne na kasa da hukumar INEC ke jagoranta tare da hadin gwiwar hukumomin zabe na jihohi. Ya kara da cewar, kwamitin tarayyar hukumomin zabe na jihohi (FOSIECON) ya fitar da sanarwa a makon da ya gabata domin tabbatar da hadin kai tsakanin INEC da hukumomin zabe na jihohi.
Alhaji Faskari ya bayyana cewar, rajistar ta fara ne daga ranar Litinin 25 ga Augusta, 2025, a cibiyoyin da aka tanada, kuma za ta ci gaba tsawon shekara guda har zuwa ranar 30 ga Augusta, 2026.
Ya jaddada cewa wadanda suka cancanci yin rajista su ne: 'Yankasa na Nijeriya, Masu shekaru akalla 18 da haihuwa, da wadanda suka cika sauran sharudda. Ya kuma yi nuni da cewar, sai wanda ke da katin zabe ne kawai zai iya kada kuri'a a zabukan shekarar 2027.
A karshe, shugaban KTSIEC ya bukaci al'ummar jihar da sauran 'yankasa baki daya da su fito kwansu da kwarkwatarsu domin yin rajista ko sabunta bayanansu na zabe.
"Ina kara kira ga dukkan wadanda suka cancanta, su daure su yi amfani da wannan dama ta rajistar katin zabe, domin ta ba su damar kada kuri'unsu a zabukan da ke tafe," in ji shi.