NOA Ta Kaddamar Da Yaki Da Munanan Bukukuwan Kammala Karatu

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes02092025_235506_FB_IMG_1756857245827.jpg

Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times 
– 2 ga Satumba, 2025

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da kyautata ɗabi'u ta Kasa (NOA) ta bayyana damuwa matuka kan yadda bukukuwan kammala karatu na dalibai ke rikidewa zuwa munanan dabi’u da rashin ɗa'a, lamarin da ta ce barazana ce ga muhimman dabi’un al’umma na ladabi, girmamawa da muntaka.

A wajen taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata a Harabar Ma’aikatar Tarayya da ke kan titin Kano Road, Katsina, Darakta Janar na NOA, Mallam Lanre Issa-Onilu—wanda Darakta na Sashen Gyaran Tsare-tsare da Inganta Ayyuka, Mista John Bala ya wakilta—ya yi kira da a dakatar da irin wannan mummunan al’ada ta bukukuwan “sign out” da ta ke kara ta’azzara.

Mista Bala ya bayyana takaici kan yadda ake ganin dalibai suna aikata rashin kunya da kuma munanan dabi’u a irin wadannan bukukuwa, ciki har da shan giya da taba, yin tsiraici a bainar jama’a, da ma yin rauni wa kansu a matsayin nuna farin ciki.

“Wasu har suna yin tsiraici, wasu shan giya da taba, wasu kuma suna yanke jikinsu suna cewa sun gama makaranta. Wannan ya sabawa dabi’unmu na gaskiya, ladabi da bin addinai biyu da muke alfahari da su,” in ji shi.

Ya kuma nuna damuwa kan yadda dalibai ke tilasta wa iyayensu su bayar da kudi don yin shagulgula, alhali ba ma sukan ga sakamakon jarabawar da suka rubuta ba.

Hukumar ta ce, a da ana daukar kammala makaranta a matsayin lokacin yin godiya da samun addu’o’in iyaye, tare da fatan alheri kan makomar karatu ko aiki, amma yanzu yin shagali da ya sabawa al’ada da addini, shi aka sa gaba

A matsayin wani bangare na aikinta na jan hankalin al’umma kan dabi’un kasa, NOA ta sanar da kaddamar da yakin wayar da kai a fadin kasar. Wannan ya hada da ziyarar makarantu, iyaye, shugabannin al’umma da kuma kafofin watsa labarai domin dakile munanan bukukuwan kammala karatu.

Mista Bala ya yi kira ga makarantu, iyaye da malamai na addinai da su hada kai domin kawo karshen wannan matsala, tare da jaddada cewa kafofin watsa labarai ma suna da rawar gani wajen fadakar da jama’a.

Wannan yaki dai wani bangare ne na shirin wayar da kan jama’a na kasa baki daya da NOA ta kaddamar a zango uku na bana wanda ya kunshi batutuwa guda biyar:

Wayar da kai kan dabi’un kasa ga matasa da dalibai.

Wayar da kai kan aikin Nigerian Identity Project da alamomin kasa.

Shirye-shiryen kauce wa ambaliyar ruwa da hadurra.

Bayani kan shirye-shiryen gwamnati kamar NELFUND da tallafin zamantakewa.

Wayar da kai kan tsaro a karkashin tsarin tsaro na Renewed Hope.

Taron da aka gudanar a Katsina ya samu halartar Daraktan NOA na Jihar Katsina, Mukhtar Lawal Tsagyam, tare da sauran daraktocin jihar da babban birnin tarayya.

NOA ta nanata cewa kiyaye ladabi da tarbiyya tsakanin dalibai hanya ce ta tabbatar da kyakkyawar makoma ga Najeriya.

Follow Us