Zaharaddeen Ishaq Abubakar | KatsinaTimes
Hukumar Wayar da Kan Jama’a ta Kasa (NOA), reshen Jihar Katsina, ta gudanar da gangamin wayar da kai a ranar Alhamis, 4 ga Agusta 2025, daga Kofar Marusa zuwa Kofar Soro a cikin garin Katsina, domin fadakar da al’umma kan tsaro, tarbiyyar dalibai da kuma girmama alamu na kasa.
Daraktan hukumar a jihar, Malam Mukhtar Lawal Tsagem, wanda ya jagoranci gangamin, ya bayyana cewa wannan shiri an tsara shi ne domin jawo hankalin jama’a kan rawar da kowa zai taka wajen tallafa wa kokarin gwamnati na tabbatar da zaman lafiya da tsaro.
“Ya zama wajibi kowane dan kasa ya kasance mai lura da harkokin tsaro, tare da kai rahoton duk wani motsi ko abin da ake zargi ga jami’an tsaro maimakon daukar doka a hannu,” in ji Tsagem.
Ya yabawa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, da sauran shugabanni bisa jajircewarsu wajen yaki da rashin tsaro, tare da yin kira ga jama’a da su yi koyi da shugabanninsu wajen kare kansu da al’ummarsu.
Daraktan ya kuma yi Allah wadai da yadda ake gudanar da bukukuwan bankwana na dalibai (sign-out) cikin rashin da’a da saba wa al’ada da addini. Ya bukaci iyaye, hukumomin makarantu da masu ruwa da tsaki da su dauki mataki wajen dakatar da wannan dabi’a.
Haka zalika, Tsagem ya yi kira ga daliban Jihar Katsina da sauran arewacin kasar nan da su yi amfani da damar shirin rancen dalibai da gwamnatin tarayya ta kaddamar, wanda ke biyan kudin makaranta kai tsaye ga jami’a tare da bai wa dalibi naira 20,000 a kowane wata. Ya ce da dama daga yankin Arewa ba su da cikakken bayani ko kuma ba su nuna sha’awa wajen yin amfani da wannan dama ba.
Daraktan ya jaddada muhimmancin girmama alamu na kasa kamar tuta da tambarin Najeriya, yana mai cewa hakan na karfafa kishin kasa da tunatar da matasa muhimmancin al’ummarsu. Ya bukaci gwamnatin jihar ta tabbatar cewa dukkan hukumomin gwamnati, makarantu da wuraren aiki na daga tutar Najeriya daidai da ka’ida.
A wani bangare na gangamin, NOA ta yi kira ga jama’a da su guji zubar da shara ko kona ta a cikin magudanan ruwa, lamarin da kan haddasa ambaliya da lalata gidaje.
Malam Tsagem ya bayyana cewa hukumar za ta ci gaba da yada wannan sakon zuwa makarantu da cibiyoyin ilimi na gaba da sakandare a fadin jihar domin tabbatar da cewa sakon ya isa kowane mataki na al’umma.
Ya gode wa manema labarai da sauran masu ruwa da tsaki da suka halarci gangamin, tare da yin kira gare su da su ci gaba da yada wannan sako domin amfanin al’ummar Katsina da Najeriya baki daya.