Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 7, Sun Jikkata 8 a Harin Magaji Wando, Dandume

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes06092025_144824_F8FpE5uWIAAM2MD.jpg


Katsina Times 

Al’ummar garin Magaji Wando da ke ƙaramar hukumar Dandume a jihar Katsina sun fuskanci mummunan hari daga ‘yan bindiga a daren Juma’a da safiyar Asabar, 5 zuwa 6 ga watan Satumba, 2025.

Shaidu daga yankin sun bayyana cewa ‘yan ta’addan sun afka wa garin inda suka kashe mutane bakwai, suka jikkata wasu takwas, sannan suka yi garkuwa da mata biyu da wani yaro. Wani rahoto ya ƙara da cewa mace guda daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su ta tsira bayan farmakin jami’an tsaro.

Wata majiya ta tabbatar da cewa al’ummar yankin sun yi ƙoƙarin ceto mutanensu, amma lamarin ya fi ƙarfin su, inda ‘yan bindigar suka ci galaba. Rahoton ya bayyana cewa Jami’an Tsaro na Katsina State Community Watch Corps (KCWC) tare da haɗin gwiwar ‘yan sanda sun isa wajen da motocin sulke domin bada ɗauki. Sai dai a lokacin da suke dawowa da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti, an yi musu kwantan bauna wanda ya yi sanadiyyar mutuwar wasu daga cikinsu da kuma ƙone musu mota.

An tabbatar da cewa an garzaya da mutum biyar zuwa Asibitin Gwamnati na Funtua, yayin da aka tura mutum uku zuwa Asibitin Katsina saboda munin raunukan da suka samu.

Hassan Shu’aibu, mai taimakawa wajen hulɗa da kafafen yaɗa labarai na gwamnatin jihar a Dandume, ya tabbatar da faruwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar.

A cikin sanarwar, ya yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ɗaukar matakan gaggawa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma, musamman ganin cewa motocin sulke sun riga sun iso domin bada kariya.

“Allah ya gafarta wa waɗanda suka rasu, ya ba waɗanda suka jikkata lafiya, sannan ya kubutar da waɗanda suke hannun masu garkuwa,” in ji sanarwar.

Lamarin ya ƙara tayar da hankula kan ci gaba da matsalar tsaro da ta addabi al’ummomin Katsina da sauran sassan Arewacin Nijeriya.

Follow Us