Katsina Times | Litinin, 15 ga Satumba, 2025
Duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla tsakanin shugabannin al’umma da ’yan bindiga a Faskari, jihar Katsina, harin kwanton bauna ya sake bayyana raunin tsarin sulhun, inda sojoji biyu suka ji rauni a sabon harin kwantan bauna da 'yan bindiga suka kai a yankin.
Rahoton Zagazola Makama ya tabbatar da cewa rakiyar kwamandan rundunar 382 Army Regiment ta fada cikin kwanton bauna a hanyar Ruwan Godiya kan titin Sheme–Kankara, lokacin da yake rangadin sansanonin sojoji a Faskari, Mabai da Dan Ali.
Ko da yake sojoji sun yi nasarar korar maharan, an tabbatar da cewa sojoji biyu sun samu rauninika, inda aka fara ba su kulawa a Mabai kafin a tura su zuwa cibiyar lafiya ta 17 Brigade.
Majiyoyi sun bayyana cewa jarumtar sojojin ta taimaka ma lamarin daga kazancewa fiye da haka. Amma harin ya zo daidai lokacin da ake ta bayyana sulhu da ’yan bindiga a matsayin hanyar kawo zaman lafiya a yankin.
Masana harkokin tsaro sun nuna cewa wannan lamari ya sake tabbatar da cewa yarjejeniyoyin sulhu da ake yi da ’yan bindiga ba su da tabbas, kuma suna ci gaba da jefa rayukan jama’a da jami’an tsaro cikin haɗari.