APC a Katsina ta fara rangadin kwanaki uku don karfafa gwiwa 'ya'yanta a shiyyar Daura.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes16092025_232918_FB_IMG_1758065284114.jpg



Auwal Isah Musa | Katsina Times 

Jam’iyyar APC mai mulkin jihar Katsina, ta kaddamar da ziyarce-ziyarce a kananan hukumomin shiyyar Daura (Daura Zone), domin tattauna batutuwa da suka shafi jam’iyyar da kuma karfafa hadin kai a tsakanin ’ya’yanta.

Ziyarar, wadda wani kwamiti na musamman da jam’iyyar ta kafa ke jagoranta, ta fara ne a ranar Talata da shafar kananan hukumomi biyar a rana ta farko, kuma za ta ci gaba na tsawon kwanaki uku.

Da yake karin haske kan manufar ziyarar a daukacin kananan hukumomin da aka ziyarta, Sakataren APC na jiha, Barista Sulaiman Namadi, ya ce akwai manyan sakonni uku da jam’iyyar ke son isarwa ga mambobinta.

Ya ce: "Na farko shi ne tabbatar da hadin kai da da’a a cikin jam’iyya tare da kare muradunta da kuma goyon bayan shugabannin jam'iyya, musamman Gwamna Dikko Radda tare da bayyana ayyukansa da kuma ba shi kariya ga mai suka. Na biyu, shi ne kaddamar da kwamitoci biyu tare da raba takardu ga masu ruwa da tsaki a kowace karamar hukuma. Sannan na uku, tabbatar da adana duk wani bayani da ya shafi harkokin jam’iyya, musamman na kudi, domin ana iya bukatarsa a gaba,” in ji shi.

Ya kara da cewar, wajibi ne kowace karamar hukuma ta rika rubuta dukkan ayyukan da gwamna, shugabannin karamar hukuma, ’yanmajalisar jiha ko Sanatan shiyyar suka aiwatar a yankinsu, domin amfanin haka a nan gaba.

Barista Namadi ya kuma bukaci shugabannin jam’iyyar su rika zama da tattaunawa da wadanda suka sauya sheka daga wasu jam’iyyu zuwa APC, tare da gargadin cewa duk wanda bai iya kare ayyukan gwamnati da jam’iyya a fili ba, ya fi dacewa ya ajiye mukaminsa ko ya fice daga jam’iyyar bisa ga a same shi yana zakon kasa ko cin duduniyar jam'iyyar.

Tawagar maziyartan, ta samu tarba daga shugabannin kananan hukumomi da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, tare da rakiyar Farfesa Lawal Charanci, Kwamishinan Harkokin Addinai na jihar, shugaban masu bukata ta musamman na jihar da sauran wasu jiga-jigai na jam’iyyar.

Kananan hukumomin da ziyarar ta shafa a ranar ta farko sun hada da: Kananan hukumomin Sandamu, Baure, Zango, Mai'adu'a da kuma Daura.

Follow Us