Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Katsina Ta Fara Bincike Kan Zargin Badakalar Kuɗaɗe ga Wasu Kansilolin jihar

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes19092025_222721_FB_IMG_1758320721744.jpg

Katsina Times 

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaki da Cin Hanci ta Jihar Katsina (KTPCACC) ta sanar da fara bincike kan wasu zarge-zargen badaƙala da barnar kuɗaɗe da ake zargin ƴan siyasa, jami’an cigaban al’umma (CDOs), da kuma wasu shugabannin makarantu a faɗin jihar.

A cikin sanarwar da Sakataren Hukumar, Dr. Jamilu M. Abdulsalam, ya fitar a ranar 19 ga Satumba, 2025, an bayyana cewa binciken ya samo asali ne daga korafe-korafen jama’a da kuma rahotanni daga hukumomin gwamnati.

Hukumar ta ce binciken farko ya nuna cewa wasu jami’an cigaban al’umma da kuma kansiloli sun karɓi kuɗaɗe daga hannun jama’a a lokacin rabon takin zamani a ƙarƙashin shirin Community Development Programme (CDP).
Adadin kuɗaɗen da ake zargin an karɓa ya kai Naira miliyan 46 da dubu 61 (₦46,061,000).

Wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma sun riga sun amsa laifin tare da fara maidowa, yayin da wasu ke cigaba da fuskantar bincike. Hukumar ta ce za ta yi duk abin da ya dace bisa doka domin dawo da kuɗin gwamnati da kuma hukunta masu hannu a ciki.

Bugu da ƙari, KTPCACC ta fara bincike kan wasu shugabannin makarantu guda huɗu daga Danja, Rimaye, Maigora da Kurami, bayan samun rahoton ma’aikatar ilimi ta jiha.
Shugabannin makarantun na fuskantar tuhumar barnatar da kuɗaɗen makarantu da suka kai ₦6,628,800, inda ɗaya daga cikinsu ake zargin ya sayar da kadarorin makaranta na dubunnaan  naira.

Haka zalika, Hukumar na gudanar da bincike a ma’aikatar Banki da Kudi ta Katsina, inda ake zargin an karkatar da kuɗi da suka kai ₦136,126,970.

Daga cikin adadin, an tabbatar da cewa an yi amfani da ₦31,800,000 bisa ka’ida, amma ₦104,326,970 ake ganin an karkatar. Zuwa yanzu, Hukumar ta bayyana cewa ta kwato ₦70,370,000, yayin da ake cigaba da ƙoƙarin kwato sauran.

Hukumar ta jaddada cewa tana gudanar da bincike cikin gaskiya da tsantseni, tare da jajircewa wajen kare dukiyar jama’a da tabbatar da gaskiya a harkokin gwamnati.

Ta kuma ƙarfafa jama’a da su cigaba da bayar da rahoton duk wata alaka da cin hanci, barnar kuɗaɗe ko yin amfani da ofis ba bisa ka’ida ba, domin tabbatar da gaskiya da zaman lafiya a Katsina.

Sunayen Wadanda Ake Zargi da Adadin Kuɗaɗen da Aka Karɓa

Jami’an Cigaban Al’umma (CDOs):

Husaini Ibrahim – ₦610,000 (Faskari LGA)

Mustapha Adamu – ₦370,000 (Faskari LGA)

Nasiru Yahaya – ₦200,000 (Faskari LGA)

Abdulkadir Sulaiman – ₦25,480,000 (Musawa LGA)

Sani Yahaya – ₦2,288,000 (Funtua LGA)

Hamza Lawal – ₦14,600,000 (Faskari LGA)

Ƴan Majalisa (Ward Councillors):

Shehu Muhammad – ₦260,000 (Dangani Ward, Musawa LGA)

Sanusi Usman – ₦125,000 (Tuge Ward, Musawa LGA)

Yusuf Nasiru – ₦126,000 (Kira Ward, Musawa LGA)

Hamza Magaji – ₦150,000 (Jikamshi Ward, Musawa LGA)

Nura Musa – ₦52,000 (Dansarai Ward, Musawa LGA)

Salisu Rabi’u – ₦112,000 (Karfi Ward, Malumfashi LGA)

Salmanu Saminu – ₦112,000 (Ruwan Sanyi Ward, Malumfashi LGA)

Lawal Hussaini – ₦300,000 (Sayaya Ward, Matazu LGA)

Ibrahim Ale – ₦250,000 (Matazu A Ward, Matazu LGA)

Aminu Abubakar – ₦200,000 (Rinjin Idi Ward, Matazu LGA)

Rufa’i Sani – ₦200,000 (Kogari Ward, Matazu LGA)

Jamilu Abubakar Muntari – ₦176,000 (Mazoji A Ward, Matazu LGA)

Ayuba Adam – ₦150,000 (Mazoji B Ward, Matazu LGA)

Falalu Sale – ₦240,000 (Gwarjo Ward, Matazu LGA)

Habib Ahmed – ₦600,000 (Matazu B Ward, Matazu LGA)


Follow Us