Katsayal Ya Bayyana Tarihin Kafa Jami’ar Sufuri ta Tarayya, Daura

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes20092025_071558_FB_IMG_1758352525018.jpg



Zaharaddeen Ishaq Abubakar 

Shugaban Jami’ar Sufuri ta Tarayya dake Daura na farko, Farfesa Umar Adam Katsayal, mni, ya bayyana irin gwagwarmayar da aka sha wajen kafa wannan cibiyar ilimi, wadda ya ce ta bambanta da kowace jami’a a Afirka.

A cikin wata tattaunawa da Katsina Time, Farfesa Katsayal ya bayyana cewa an samar da jami’ar ne sakamakon yarjejeniyar aikin layin dogo daga Legas zuwa Kano tsakanin Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya da Kamfanin Gine-ginen Kasar Sin, CCECC.

“Ba wai kawai an kafa jami’ar ne don ƙara yawan jami’o’i a ƙasar ba. An kafa ta ne saboda bukatar samun kwararrun ma’aikata da za su tafiyar da aikin zamani na layin dogo. Idan babu wannan horon, aikin gyaran layin dogo zai gamu da cikas,” in ji shi.

Ya ce tun farko an yi niyyar kafa cibiyar koyon harkokin layin dogo, amma daga baya aka faɗaɗa ra’ayin zuwa ga dukkan fannoni na sufuri,  jirgin ƙasa, hanya, ruwa da jirgin sama abin da ya sa ta zama Jami’ar Sufuri ta Tarayya.

Farfesa Katsayal ya kuma bayyana cewa an gina jami’ar ne ta hanyar tsarin Corporate Social Responsibility (CSR) to da aka tsara ta hanyar yarjejeniya da CCECC.

“Ba kuɗi suka bayar ba. Gwamnati ta samar da filin, su kuma suka amince su gina gine-ginen a sassa bisa ga yadda ake biyan su daga aikin layin dogo,” in ji shi.

Dangane da ƙalubale, ya ce tun da aka fara, jami’ar ba ta da kasafin kuɗi, kuma shi kaɗai aka nada a matsayin shugaban jami’a ba tare da sauran jami’an gudanarwa ba.

“Ni kaɗai nake aiki daga matsayin shugaban jami’a har zuwa ma’aikaci mai rubutu. Ni nake rubuta wasiƙa, na buga, na kai, na kuma bi sawu. Wani lokaci har barci nake yi a cikin mota a Abuja saboda gajiya, sai da safe na ci gaba da aiki. Wannan ya faru ne bayan albashina daga tsohuwar jami’a ta tsaya, amma a nan babu ma albashi saboda ba a ware kasafin kuɗi ba,” in ji shi.

Sai dai duk da wahalhalu, Farfesa Katsayal ya ce yana ganin wannan aikin a matsayin wata dama ta musamman wajen taimaka wa ci gaban ƙasa.

“Wannan wani babban aiki ne na ƙasa da zai shafi duniya gaba ɗaya. Kafa jami’a daga tushe ba abu ne mai sauƙi ba, amma yana da gagarumin amfani,” ya ƙara da cewa.

Jami’ar Sufuri ta Tarayya, Daura, ita ce ta farko a Afirka da aka tsara musamman domin samar da ƙwararru a fannonin sufuri.

Wannan labarin wani ɓangare ne na tattaunawar Katsina Time da Farfesa Umar Adam Katsayal, mni, Shugaban Jami’ar Sufuri ta Tarayya, Daura.

Don cikakkiyar tattaunawar a harshen Turanci, ku biyo mu a Katsina Time TV a YouTube da sauran kafafen sada zumunta.

Follow Us