@ katsina times
Mutane daban daban sun bayyana yadda suka ga fulanin daji masu dauke da makamai yadda suka shigo kasuwar Dutsinma a jiya laraba 1 ga watan oktoba wadda take ranar kasuwa ce.
Jama a sun ce sun shigo kasuwar ne, bayan zaman sasancin da akayi karshen satin da ya gabata. Ganau sun fada ma jaridun katsina times cewa sun shigo garin ta hanyoyi daban daban bisa mashinan su.
Ganau sunce sun shigo a cikin yunwa duk inda suka ga mai nama ko burodi da lemu' in suka tsaya sai sun koshi.ganau sun ce sun kuma rika bin kasuwar suna sayen abin bukata.
Ganau sun ce ba wanda ya shigo da makami a bayyane, kuma basu cin fuska ko tozarci ga kowa .
" Daka gansu kasan dajin ya ishe su kuma suna a cikin bukatar kayan abinci,Dana more rayuwa" inji wani dake bayyana ma jaridun katsina times yadda ya gansu.
Ganau sunce sun hadu a inda suka ajiye baburansu bayan la asar, kowa da kaya niki niki.sannan kamar sunyi ma junansu signal duk suka hanya zuwa komawa daji a cikin gungu.
Ganau sunce mutanen gari sun gane da yawa daga cikin su, illa kawai sun dade ba a gansu cikin gari ba, ashe suna daji.
Ganau sun ce wani yaga wani tsohon abokinsa da suka rabu shekaru biyar da suka wuce, ashe yana daji ya zama karamin kwamanda.aka ce suka taba hannu suka rungume Juna.ya tambaye shi kana ina yace ina daji tsakanin zamfara da katsina.
Yadda aka ga fulanin daji a kasuwar Dutsinma a jiya ta tabbata mutanen nan suna son sulhu koda kuwa na wucin gadi ne..domin shigar da kayan bukatu a daji.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page/ group:katsina city news
Da sauran shafukan sada zumunta
07043777779( whazzapp only)