ASUU Jami'ar Umaru Musa ta Bai wa Dalibai Masu Karamin Karfi da Nakasa Tallafin Karatu

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes16102025_175418_FB_IMG_1760637194283.jpg



Daga wakilinmu a Katsina 

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) reshen Jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU) ta bai wa wasu dalibai masu ƙaramin ƙarfi da kuma dalibai masu nakasa tallafin karatu a wani shiri da take gudanarwa duk shekara domin tallafa wa al’umma.

Taron bayar da tallafin ya gudana ne a ranar Alhamis, 16 ga Oktoba, 2025, a ofishin ASUU da ke cikin jami’ar, karkashin jagorancin Dr. Murtala Abdullahi Kwara, shugaban ƙungiyar ta ASUU-UMYU.

A cewar Dr. Kwara, wannan shiri na tallafin karatu wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙungiyar wajen inganta ilimi da tallafa wa daliban da ke fuskantar matsin tattalin arziƙi.

Ya bayyana cewa kungiyar ASUU ta ƙasa ta ƙara yawan kuɗin tallafin daga ₦100,000 zuwa ₦200,000 ga kowane dalibi, tare da umartar kowanne reshe ya zaɓi dalibai biyu da suka cancanta. “Bayan wannan, reshenmu na jami’ar UMYU ya ƙara wasu dalibai uku da za su amfana, bisa la’akari da halin matsin tattalin arziƙi da ake ciki yanzu,” in ji shi.

Dr. Kwara ya kuma bayyana cewa tawagar shugabannin na ASUU na ƙasa (NEC) sun ziyarci jami’ar domin tattaunawa da gwamnatin jihar Katsina kan batutuwan da suka shafi ƙungiyar.

Shugaban kwamitin tantance masu cin gajiyar tallafin ya bayyana cewa an gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci, inda aka duba halin rayuwa da kuma ƙwarewar karatun daliban. Ya ce, sharuɗɗan sun haɗa da kasancewa ɗan ƙasa mai ƙaramin ƙarfi tare da samun CGPA mafi ƙaranci 3.50.

Waɗanda suka samu tallafin ASUU na ƙasa sun haɗa da: Sakina Abdullahi, ɗaliba a matakin 300 a sashen Larabci, da Fatima Musa Mahuta, ɗaliba a matakin 300 a sashen Kimiyyar Kwamfuta mai CGPA 4.16.

Waɗanda suka ci gajiyar tallafin ASUU-UMYU kuma sun haɗa da: Fatima Mustafa, ɗaliba mai nakasa a sashen Special Education (CGPA 3.50),Muhammad Ahmad, ɗalibi mai nakasa a sashen Special Education (CGPA 3.67), da
Binta Mahamad, ɗaliba a sashen Lissafi (CGPA 3.82).

Dr. Kwara ya yaba wa daliban bisa jajircewarsu, yana mai ƙarfafa su da su ci gaba da himma a karatu, domin ilimi shi ne ginshiƙin ci gaban ƙasa.

Ya kuma tabbatar da cewa ASUU za ta ci gaba da tallafawa marasa galihu da dalibai masu nakasa a matsayin gudummawar ƙungiyar ga al’umma da ci gaban jami’o’in gwamnati a Najeriya.

Follow Us