Katsina Times
Kungiyar nan mai rajin hadin kan 'yan Nijeriya da dunkulewarsu, 'Nigeria First Project Initiative' a turance, ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su guji shiga zanga-zangar da wasu ke shirya wa domin neman sakin shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu, tana mai cewar sakinsa zai iya kara haifar da tashin hankali da kuma sake tayar da rikice-rikice a fadin ƙasar.
Kungiyar a ta bakin babban Ko'dinetanta na Kasa, Kwamared Hamza Umar Saulawa ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ta kira a ranar Litinin a jihar Katsina.
Kwamared Hamza Umar Saulawa, ya ce kungiyar ta damu matuka bisa ga irin sakonnin ƙiyayya da rarrabuwar kawuna da Kanu ke yadawa, tun bayan tserewarsa daga ƙasar a 2017 bayan ya karya sharuɗɗan Beli da kotu ta ba shi.
“Kanu ya tsere zuwa ƙasashen waje inda ya ci gaba da aikawa da sakonni na tayar da hankali da ƙiyayya ta kafafen sada zumunta da Radio Biafra, abin da ya janyo mutuwar jami’an tsaro da daruruwan ‘yan Nijeriya,” in ji sanarwar.
Kungiyar ta ce sake ba wa Kanu damar fita daga hannun hukuma zai zama barazana ga tsaron ƙasa da haɗin kan 'yan Kasar, musamman ganin yadda ƙungiyarsa ta IPOB ta kafa dokar “zaman gida” a yankin Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu, wadda ke janyo wa jama’a wahala da durƙushewar harkokin kasuwanci har ma da na ilimi.
Kungiyar ta ci gaba da cewar, tun bayan sake kama Kanu a shekarar 2021, kotu ta ƙi amincewa da roƙonsa na sake samun Beli saboda, a cewar ƙungiyar, akwai dalilai masu ƙarfi da ke nuna zai sake guduwa idan aka sake shi.
“Idan aka sake sakinsa, babu shakka zai ci gaba da yada ƙiyayya, tashin hankali da kalaman da ke nufin ƙalubalantar ikon gwamnatin Nijeriya,” in ji ta.
A ta bangare guda, Kungiyar ta yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa matakin da ya ɗauka na ba wa ‘yan Nijeriya 175 afuwa a ƙarƙashin ikon shugaban ƙasa na 'Prerogative of Mercy', tana mai cewar hakan ya nuna shugaban ba ya da ƙiyayya da kowa, kuma yana son ba wa waɗanda suka nuna nadama dama ta biyu.
“Shugaban ƙasa yana kokarin gina ƙasa ta hanyar adalci da bin doka, ba tare da tsoma baki cikin shari’o’in masu laifin ta’addanci ko cin amanar ƙasa ba,” Sanarwar ta jinjina wa shugaban kasar.
Hakazalika, Kungiyar ta kuma yi Allah-wadai da jita-jitar juyin mulki da ake yadawa kwanan nan, tana mai cewar makirci ne na wasu ‘yanƙasa masu son tarwatsa demokaradiyyar Nijeriya da aka gina cikin shekaru 26 ba tare da yankewa ba.
“Demokaradiyyar Nijeriya tana cikin koshin lafiya. Ta yi ƙarfi, kuma tana ci gaba da bunƙasa. Sai masu son mulkin kama-karya da masu tayar da fitina ne kawai za su so a lalata wannan nasara,” in ji Sanarwar da Saulawa ya fitar.
A nata bangare, kungiyar, ta bayyana cikakken goyon bayanta ga tsarin mulkin demokaradiyyar da ke gudana yanzu, tana mai cewar babu barazana ko wata shegantakar da za ta iya tarwatsa demokaradiyya a Nijeriya. Ta kuma yaba wa gwamnatin Tinubu bisa ƙoƙarin ƙarfafa tattalin arziki, daidaita kudin musaya, da gyaran tsarin haraji domin bunƙasa harkokin kasuwanci da noman zamani.
A ƙarshe, ƙungiyar ta sake nanata cewar sakin Nnamdi Kanu fa a halin yanzu zai iya zama hatsari ga tsaron ƙasa, tana mai kara kira ga duk masu kishin Nijeriya da su guji shiga zanga-zangar #FreeNnamdiKanu da ake shirya wa a wasu sassan ƙasar.
Taron manema labaran fai ya samu bayyanar Daraktan bincike da tsare-tsare na kungiyar, Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa da sauran membobin kungiyar na jiha, Katsina Times da sauran 'yanjarida.