Daga Katsina Times
Katsina — Laraba 28 Janairu 2026
Wasu jami’an tsaro da ake zargin suna aikin kula da ginin tagwayen hanyoyi daga Kofar Soro zuwa Kofar Sauri sun harbe wani yaro mai suna Zakariyau Ibrahim Kashiya a birnin Katsina.
Binciken da Katsina Times ta gudanar ya nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata da misalin karfe 1:00 na rana, a kusa da kwanar Asibiti daga Kofar Soro. Bayan harbin, an gaggauta daukar Zakariyau zuwa Asibitin Koyarwa na Jihar Katsina domin samun kulawar gaggawa.
Sai dai, rahotanni sun bayyana cewa Zakariyau ya rasu da misalin karfe 11:00 na dare a sakamakon rashin samun kulawar da ta dace.
An shirya gudanar da jana’izarsa da misalin karfe 11:00 na safiyar yau Alhamis.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, rundunar ’yan sanda ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba. Kokarin da Katsina Times ta yi na jin ta bakin jami’an tsaron da abin ya shafa bai yi nasara ba.