Dikko Project Movement Ta Bayyana Goyon Bayan Tinubu Da Raɗɗa A Zaɓen 2027

Kungiyar Dikko Project Movement ta sanar da amincewarta tare da bayyana cikakken goyon bayanta ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Asiwaju....

Katsina City News February 01, 2026  ·  12:00 AM
| 625 Views


Kungiyar Dikko Project Movement ta sanar da amincewarta tare da bayyana cikakken goyon bayanta ga Mai Girma Shugaban Ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da kuma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Kungiyar ta bayyana wannan matsaya ne a wata sanarwa da shugabanta, Hon. Musa Yusuf Gafai, ya fitar a ranar Asabar, inda ya jaddada cewa goyon bayan ya samo asali ne daga abin da ya kira shugabanci nagari da manufofin ci gaba da shugabannin ke aiwatarwa a matakin ƙasa da jiha.

A cewar sanarwar, Dikko Project Movement za ta shiga sahun gaba tare da dukkan rassanta da mambobinta domin haɗa kai da sauran ƙungiyoyi masu kishin ci gaba, da nufin tabbatar da cewa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta samu nasara a kowane mataki na zaɓe mai zuwa.

Kungiyar ta kuma bayyana ƙudurin ta na wayar da kan jama’a da ƙarfafa haɗin kai tsakanin magoya bayan jam’iyyar domin cimma nasarar zaɓe cikin lumana da bin doka da oda.

Sanarwar ta ƙare da kira ga al’umma da su ci gaba da mara wa shugabanni baya domin dorewar zaman lafiya, cigaba da kwanciyar hankali a Jihar Katsina da Najeriya baki ɗaya.

Advertisement

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 1 + 3?