MUMMUNAR GOBARA A WAJEN AIKIN MA'ADAINAI A NAHUTA TA CINYE DUKIYOYIN MILIYOYIN NAIRORI

......Akwai asar rayuka.Wata mummunar gobara da ta tashi a wajen da ake aikin nikan zinare a garin Nahuta ta karamar....

Katsina City News March 08, 2026  ·  12:00 AM
| 603 Views
......Akwai asar rayuka.

Wata mummunar gobara da ta tashi a wajen da ake aikin nikan zinare a garin Nahuta ta karamar hukumar Batsari jihar Katsina, ta lakume dukiyoyin yan kasuwa na miliyoyin nairori.

Lamarin ya fara da sanyin safiyar yau lahadi 08-03-2026, inda aka wayi gari da iftila'in tashin gobara wacce ta buwayi  jamaa wajen dakatar da ita.

Ana zargin cewa wani murhun girki na zamani ne sanadiyyar tashin wannan gobara wacce har ya zuwa hada rahoton nan baa iya tantance yawan asarar da aka tafka ba sanadiyyar tashin gobarar. Da yake wajen an kawata shi da shaguna da runfunan kara da sauran kayansu wanda dukkansu dauke suke da kayan sayarwa. 

Baya ga asarar dukiya, an bayyana cewa wutar ta yi sanadiyyar mutuwar mutum daya wanda majiyar mu ta bayyana cewa lokacin da wutar ta kama yana barci, anyi kokarin ceto shi amma abun ya gagara, dole aka hakura kaddara ta riga fata.

Advertisement

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 6 + 9?