@ katsina times
Wasu da ake zargin tubabbun ƴan bindiga ne ma su garkuwa da mutane sun tare wasu ƴan mata a hanyar Batsari zuwa Yasore, mai
nisan kilomita 3 daga Batsari, hedikwatar ƙaramar hukumar Batsari ta jahar Katsina.
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 07:30pm yamma ranar alhamis 19-03-2026, inda ɓarayin suka tsaya daidai magamar hanyar Yasu-yasu da Yasore, sun laɓe cikin itacen mangwaro. Lokacin da ƴan matan suka iso sai ɓarayin suka fito suka nufe su da nufin kama su. Da suka farga sai suka tarwatse kowa yayi ta kansa. Sun yi sa'ar kama ɗaya daga cikin ƴan matan, suka tafi da ita har wajen Ɗangeza suka ƙwace wayar hannu, kuɗi N8000 da kayan da ta sawo daga kasuwa.
Nan da nan labari ya bazu cikin karkara, muta ne suka fito ta ko'ina domin kawo ɗauki, ganin haka yasa suka sake ta, domin su tsira.
Haka kuma labarin ya kai ma tubabben ɗan bindiga Abu Raɗɗe, wanda take ya turo yaran sa, suka bazama neman su, amma sun riga sun ɓuya. Amma wata majiya ta bayyana cewa an gane su kuma tuni a tsegunta ma Abu Raɗɗe.