Ƴan Bindiga Sun Sace Maigarin Kogari Da Wasu Mata A Ƙaramar Hukumar Matazu

A daren ranar Talata, 12 ga watan Mayu, 2027, wasu ’yan bindiga ɓarayin daji sun kai hari garin Kogari da....

Katsina City News May 13, 2026  ·  12:00 AM
| 309 Views


A daren ranar Talata, 12 ga watan Mayu, 2027, wasu ’yan bindiga ɓarayin daji sun kai hari garin Kogari da ke Ƙaramar Hukumar Matazu, inda suka yi garkuwa da Maigarin garin, Bello Abdulkarim, tare da ’yarsa.

Maharan sun kuma sace matar wakilin maigarin tare da ’yarta, baya ga wasu mata biyu da suka ɗauka daga cikin garin.

Rahotanni sun ce harin ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba da tashin hankali.

Al’umma sun yi addu’ar Allah Ya kuɓutar da waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya da aminci.

Advertisement

Tags: A Daren...

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 2 + 9?