AN SAMU RAHOTANNI 105 NA BULLAR SANKARAU A JIHAR KATSINA

Daga Garba Abu Abdullahi Jikamshi A yayin da arewacin Najeriya ke cigaba da fuskantar yanayin zafi, Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar....

Katsina City News May 14, 2026  ·  12:00 AM
| 1,670 Views
Daga Garba Abu Abdullahi Jikamshi 

A yayin da arewacin Najeriya ke cigaba da fuskantar yanayin zafi, Gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da samun rahotanni 105 na bullar cutar sankarau.

An samu rahotannin bullar cutar ne daga kusan kananan hukumomi 20 da ke a jihar.

Wannan na zuwa ne daga Shugaban Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko Dr Shamsuddeen Yahaya, a yayin jawabi ga manema labaru.

Ya ce ba a tabbatar da rahotannin ba har sai an gudanar da gwaje-gwaje tukunna.

Sai dai Kuma majiyyatan da su ka yi korafin tsananin ciwon Kai ko makalewar wuya na samun kulawar gaggawa.

Ya tabbatar da cewa jihar Katsina na cigaba da matsa kaimi wajen lura da sanya ido a kan wannan barazana, ya na Mai cewa an Samar da wata cibiyar gaggawa da ke aiki dare da rana don Kai dauki a yayin da bukatar hakan ta taso

Advertisement

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 9 + 1?