Hukumar Hana Fasakwabri Da ‘Yan Jarida Sun Ƙarfafa Haɗin Gwiwa a Taron Shiyyar Kano/Jigawa

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes26052026_210648_FB_IMG_1779829533211.jpg

Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar



Hukumar hana Fasakwabri ta kasa, Nigeria Customs Service (NCS) ta jaddada kudirinta na ƙarfafa haɗin gwiwa da kafafen yaɗa labarai a Arewacin Najeriya domin inganta wayar da kan jama’a, sauƙaƙa harkokin kasuwanci, tsaron kan iyaka da ci gaban ƙasa.

An bayyana hakan ne a wani taron ganawa da manema labarai da hukumar ta shirya wa shiyyoyin Zone B a Kano, wanda ya haɗa jami’an hulɗa da jama’a na Kwastam da ‘yan jarida daga jihohin Kano, Katsina, Jigawa da Kaduna.

Taron wanda aka gudanar a zauren taro na Kano/Jigawa Area Command da ke titin Sani Marshall a Bompai, Kano, ya gudana ne ƙarƙashin taken: “Gina Haɗin Gwiwa Tsakanin Kafofin Yaɗa Labarai da Hukumar Kwastam Domin Ƙara Wayar da Kan Masu Ruwa da Tsaki da Ci gaban Ƙasa.”

Da yake jawabi a wajen taron, Kakakin Hukumar Kwastam ta Ƙasa, Abdullahi Aliyu Maiwada, ya bayyana cewa hukumar tana kallon kafafen yaɗa labarai a matsayin abokan hulɗa masu muhimmanci wajen inganta gaskiya, riƙon amana da wayar da kan jama’a.

Maiwada, wanda ya yi jawabi a madadin Shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, Bashir Adewale Adeniyi, ya yaba wa ‘yan jarida bisa ci gaba da goyon baya da kuma yadda suke wallafa ayyukan hukumar a faɗin ƙasar nan.

Ya ce hukumar ta ga dacewar faɗaɗa hulɗarta da ‘yan jarida daga yankin Arewa bayan ta dade tana mai da hankali kan ‘yan jaridun harkokin tashoshin jiragen ruwa da ke Legas da Fatakwal.

A cewarsa, yada rahotonnin Kwastam yana da matuƙar buƙatar fasaha da buƙatar horas da ‘yan jarida domin su fahimci manufofin kasuwanci, sauƙaƙa cinikayya da kuma kalmomin fasaha na hukumar.

“Mun fahimci akwai gibi wajen fahimtar wasu muhimman kalmomi da manufofin harkokin Kwastam. Dole ne a fara ilmantar da ‘yan jarida kafin su iya sanar da jama’a yadda ya kamata,” in ji shi.

Maiwada ya bayyana cewa hukumar na shirin shirya horaswa ta musamman ga ‘yan jaridar da ke bibiyar harkokin Kwastam da kasuwanci domin inganta rahotanni da fahimtar jama’a kan sauye-sauyen da ake aiwatarwa a hukumar.

Ya ƙara da cewa Hukumar Kwastam na ci gaba da aiwatar da manyan sauye-sauye a ƙarƙashin jagorancin shugaban hukumar, musamman a fannin zamani na kasuwanci, amfani da fasahar sadarwa da kuma ƙara bayyana gaskiya a ayyukanta.

Kakakin ya ce an kai wasu ‘yan jarida da suka halarci horaswa a Abuja rangadin cibiyoyin bayanai da ofisoshin gudanar da ayyukan fasaha na hukumar domin su ga irin ci gaban da ake samu a bangaren fasahar zamani.

Ya jaddada cewa isar da sahihan bayanai cikin lokaci na da matuƙar muhimmanci wajen nasarar manufofin hukumar, yana mai cewa masu shigo da kaya, masu fitar da kaya, dillalan Kwastam, masana’antu da al’ummomin kan iyaka duk suna dogaro ne da ingantattun bayanai.

Maiwada ya kuma sanar da shirin kafa wata kafa ta sadarwa ta musamman ga ‘yan jaridar Arewa domin sauƙaƙa hulɗa kai tsaye tsakanin ‘yan jarida da jami’an hulɗa da jama’a na Kwastam a yankin.

Haka kuma ya bayyana irin haɗin gwiwar da hukumar ke da shi da kafafen yaɗa labarai, musamman waɗanda ke amfani da harshen Hausa a Arewa.

A cewarsa, hukumar na da alaƙa ta aiki da kafafe irin su Federal Radio Corporation of Nigeria (FRCN), Voice of Nigeria, Trust TV, TVC da Nigerian Television Authority (NTA), da sauran kafafe.

Tun da farko, Mukaddashin Kwanturola na shiyyar Kano/Jigawa Area Command, Usman Umar Adamu, ya bayyana kafafen yaɗa labarai a matsayin gada tsakanin hukumomi da jama’a.

Ya yabawa Maiwada bisa ƙaddamar da taron, yana mai cewa haɗin gwiwa tsakanin Kwastam da ‘yan jarida na da matuƙar muhimmanci wajen sadarwa da hulɗa da masu ruwa da tsaki.

Adamu ya tabbatar wa ‘yan jarida cewa ƙofarsa a buɗe take domin karɓar shawarwari da kuma tattauna batutuwan da suka shafi ayyukan hukumar.

A nasa jawabin maraba, jami’in hulɗa da jama’a na Shiyya (Zone B, Kano/Jigawa Area Command), T. Y. Balarabe, ya ce an shirya taron ne domin ƙarfafa tattaunawa, fayyace ayyukan Kwastam da kuma inganta haɗin gwiwa da kafafen yaɗa labarai.

Shi ma shugaban kungiyar 'yan jarida (Nigeria Union of Journalists) (NUJ) na Kano, wanda mataimakinsa ya wakilta, ya yaba wa Hukumar Kwastam bisa shirya taron a Kano.

Ya ce alaƙar da ke tsakanin Kwastam da kafafen yaɗa labarai na da anfani ga ɓangarorin biyu, yana mai cewa samun sahihan bayanai da aikin jarida na gaskiya suna taimakawa wajen yaƙi da yaɗa bayanan ƙarya da kuma ƙarfafa amincewar jama’a.

Taron ya samu halartar ‘yan jarida daga kafafe daban-daban na Arewa maso Yamma ciki har da Katsina Times, News Agency of Nigeria, Daily Trust, Arise Television, Leadership Hausa, Vision FM Katsina da Alfijir Radio Katsina.

An kuma gudanar da zaman tattaunawa tsakanin jami’an Kwastam da ‘yan jarida kan wayar da kan jama’a, sadarwa ta hukumomi da hanyoyin ƙara fahimtar juna tsakanin hukumar da kafafen yaɗa labarai a yankin.

Follow Us