CIWON ZUCIYA NE SANADIN RASUWAR ABACHA, BA GUBA BA

Daga Garba Abu Abdullahi Jikamshi Tsohon Mataimakin Director a hukumar Yansandan Ciki (DSS), Dennis Amachree ya bayyana cewa bugawar zuciya ne....

Katsina Times June 11, 2026  ·  12:00 AM
| 183 Views
CIWON ZUCIYA NE SANADIN RASUWAR ABACHA, BA GUBA BA
CIWON ZUCIYA NE SANADIN RASUWAR ABACHA, BA GUBA BA


Daga Garba Abu Abdullahi Jikamshi 

Tsohon Mataimakin Director a hukumar Yansandan Ciki (DSS), Dennis Amachree ya bayyana cewa bugawar zuciya ne sanadin rasuwar tsohon shugaban mulkin soja Janar Sani Abacha, ba wai guba ba kamar yadda a ke yadawa.

Dennis Amachree ya ce mafi yawan rahotannin da a ke bazawa dangane da musababbin rasuwar tsohon shugaban Kasar na mulkin soja, jita-jita ce da labarun kanzon kurege.

Tsohon Jami'in Tsaron ya bayyana cewa dukkanin sakamakon bincike da a ka gudanar, ya tabbatar da cewa bugawar zuciya ne sanadiyyar rasuwar Abacha, sabanin maganganun da ke yaduwa bakunan mutane.

Dennis Amachree dai ya bayyana hakan ne a wani bangare na littafin da ya wallafa, da Kuma hirar da a ka yi da shi a tashar talbijin ta TVC.

Advertisement

Written by

Katsina Times

Katsina Times is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 8 + 1?