Jiga-Jigan ADC a Katsina Sun Nuna Damuwa Kan Rikicin Cikin Gida, Sun Shirya Taron Neman Mafita da Kafa Kwamitin Makomar Jam'iyyar.

Daga Auwal Isah Musa |  Katsina TimesWasu manyan jiga-jigan Jam’iyyar ADC da magoya bayansu ƙarƙashin jagorancin Alhaji Salisu Sallau Arawa sun gudanar da wani taro na musamman mai taken “Katsina…

Katsina City News June 21, 2026  ·  12:00 AM
| 52 Views
Jiga-Jigan ADC a Katsina Sun Nuna Damuwa Kan Rikicin Cikin Gida, Sun Shirya Taron Neman Mafita da Kafa Kwamitin Makomar Jam'iyyar.
Jiga-Jigan ADC a Katsina Sun Nuna Damuwa Kan Rikicin Cikin Gida, Sun Shirya Taron Neman Mafita da Kafa Kwamitin Makomar Jam'iyyar.

Daga Auwal Isah Musa |  Katsina Times

Wasu manyan jiga-jigan Jam’iyyar ADC da magoya bayansu ƙarƙashin jagorancin Alhaji Salisu Sallau Arawa sun gudanar da wani taro na musamman mai taken “Katsina Ina Makoma?”, inda suka tattauna halin da siyasar adawa ke ciki a Jihar Katsina tare da neman hanyoyin ceto makomar jam’iyyar da jihar baki ɗaya.


Taron, wanda ya samu halartar shugabanni da wakilai daga shiyyoyin Katsina, Daura da Funtua, ya mayar da hankali ne kan matsalolin rashin haɗin kai da rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyun adawa, lamarin da mahalarta taron suka ce na ci gaba da raunana ƙoƙarin kawo sauyi a jihar.


Da yake jawabi a wajen taron, jagoran taron kuma shugaban ayarin neman mafita, Alhaji Salisu Sallau Arawa, ya bayyana cewa babban dalilin shirya taron shi ne duba makomar siyasar adawa a Katsina, musamman bayan abin da ya bayyana a matsayin gazawar shugabanni wajen haɗa kan mabiyansu.


Ya ce duk da irin sadaukarwar da mambobin jam’iyyar suka yi da fatan samar da canji, sun wayi gari suna fuskantar ruɗani da rashin tabbas kan alkiblar da shugabannin siyasa ke kaiwa.


“Mun shiga siyasa ne da niyyar kawo canji, amma abin takaici shugabanninmu sun kasa ba mu jagoranci mai ma’ana. Kullum sai an ji sabbin labarai masu karo da juna a kafafen yaɗa labarai, har mambobi ba su san inda aka dosa ba,” in ji shi.


Alhaji Sallau ya tunatar da yadda aka kafa wata ƙungiya a ƙarƙashin ADC da ta haɗa matasa da dattawa daga kowane gunduma, inda aka tattara mutane 50 daga kowace mazaɓa ba tare da an bai wa kowa kuɗi ba. Ya ce duk da irin wannan kishin jihar da jam’iyya, yau da yawa daga cikin waɗannan mutane sun rasa sanin matsayinsu saboda rikice-rikicen da suka dabaibaye jam’iyyar.


Sai dai ya jaddada cewa taron ba a shirya shi ne domin sanar da ficewa daga ADC ko komawa wata jam’iyya ba, illa domin tattaunawa kan makomar siyasa da yadda za a samar da mafita ga mambobi da al’ummar jihar.


Advertisement

“Ba mu zo nan domin mu sanar da komawa wata jam’iyya ba. Mun zo ne domin mu tattauna makomarmu a matsayinmu na ’yan Katsina masu kishin jihar da kuma masu ruwa da tsaki a siyasar jihar,” ya bayyana.


Ya kuma soki yadda ake tafiyar da jam’iyyun adawa a Najeriya, yana mai cewa abin ya koma tamkar wasan kwaikwayo, inda wasu shugabanni ke yin kalaman gyara da adalci a fili amma ayyukansu ba sa nuna hakan.


A cewarsa, rikicin da ya dabaibaye ADC ya kai matakin da ake da masu iƙirarin muƙamai iri biyu a fannoni daban-daban, ciki har da ’yan takarar gwamna, sanatoci, majalisun tarayya da na jiha, har ma da shugabannin jam’iyya a wasu ƙananan hukumomi, yana mai bayyana hakan a matsayin ci amanar mambobin da suka yi imani da manufar jam’iyyar.


Haka kuma, Sallau ya nuna damuwa kan matsalolin tsaro da ke addabar wasu sassan Kudancin Katsina da Kudu maso Yammacin jihar, yana mai cewa al’umma na rayuwa cikin fargaba sakamakon hare-haren da ake yawan samu.


Ya bayyana fatan cewa kwamitin da za a kafa bayan taron zai taimaka wajen samar da sahihiyar mafita da sabuwar alkibla ga masu siyasar adawa a jihar.


A ƙarshen taron, mahalarta sun amince da kafa wani kwamitin matasa da wakilan yankuna domin gudanar da bincike, tattara ra’ayoyi da kuma gabatar da shawarwari kan makomar siyasar adawa a Jihar Katsina.


Taron ya samu halartar fitattun jiga-jigan siyasa da suka haɗa da Dr. Sani Lawal Daura, Farfesa Abubakar Babaje, Barrista Usman Buhari Danja, Hajiya Rayyanatu da Hajiya Hadiza Muhammad da sauransu, waɗanda suka bayar da gudummawar ra’ayoyi kan hanyoyin da za a bi wajen ƙarfafa haɗin kai da samar da sahihiyar mafita ga jam’iyyun adawa.


Masu jawabi a taron sun jaddada cewa haɗin kai da tsayayyen shugabanci ne kaɗai za su iya bai wa jam’iyyun adawa damar ƙalubalantar jam’iyya mai mulki da kuma samar da sauyin da al’ummar Katsina ke fata a zaɓuɓɓuka masu zuwa.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 8 + 9?