Daga Mu'azu Hassan, Katsina Times
Rahotanni daga majiyoyi mabambanta sun tabbatar wa da Katsina Times cewa an kusa kammala cimma matsaya tsakanin jagoran adawa a Jihar Katsina, Dakta Mustapha Muhammad Inuwa, da tsagin Jam'iyyar PDP mai biyayya ga Tanimu Turaki.
Majiyoyin sun bayyana cewa an shafe kwanaki ana gudanar da tattaunawa tsakanin Dakta Mustapha Inuwa da manyan jiga-jigan PDP na tsagin Turaki, inda a ƙarshe aka cimma yarjejeniya kan muhimman batutuwa.
Bisa ga bayanan da aka samu, yarjejeniyar ta tanadi bai wa Dakta Mustapha Inuwa cikakken iko kan harkokin jam'iyyar a Jihar Katsina a ƙarƙashin wannan tsagi. Wannan iko ya haɗa da naɗa shugabannin jam'iyyar tare da zaɓen masu neman takara daga matakin ɗan Majalisar Jiha har zuwa kujerun Sanata.
Majiyoyinmu sun kuma tabbatar da cewa Dakta Mustapha Inuwa ya amince da karɓar takarar gwamnan Jihar Katsina a ƙarƙashin wannan tsagin na PDP.
Ana sa ran Dakta Mustapha Inuwa zai yi taro da magoya bayansa a cikin wannan mako ko kuma farkon mako mai zuwa domin sanar da su matsayar da ya ɗauka.
Idan wannan rahoto ya tabbata, Jam'iyyar PDP a Jihar Katsina za ta kasance da masu neman takarar gwamna biyu, wato Sanata Yakubu Lado da Dakta Mustapha Inuwa. Haka kuma, Jam'iyyar ADC ma tana da masu neman takarar gwamna biyu, Sanata Ahmed Babba Kaita da Alhaji Salisu Lawal Uli.
Har ila yau, majiyoyinmu sun bayyana cewa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bai wa dukkan jam'iyyun siyasa da ke da shari'o'i a kotu damar shiga tsarin adana bayanan hukumar domin gabatar da sunayen 'yan takararsu. Sai dai daga ƙarshe, hukuncin kotu ne zai tantance tsagin da INEC za ta amince da shi tare da aiki da sunayen 'yan takarar da ya gabatar.
A cewar majiyoyin, tsagin PDP na Tanimu Turaki na da damar miƙa sunayen 'yan takararsa ga INEC, kasancewar lokacin ƙarshe na tantance sunayen bai cika ba, kuma har yanzu kotu ba ta yanke hukunci kan rikicin cikin jam'iyyar ba.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Facebook. Katsina city News
Facebook. Jaridar Taskar labarai
Katsina times @ all social media handles


Comments (0)
No comments yet. Be the first to share your thoughts!