El-Rufai ya Nemi Afuwar Kotu Bayan ya Janye Wasu Bukatu Uku

Lauyan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wato Barista Paul Erokoro (SAN), ya bai wa Babbar Kotun Jihar Kaduna haƙuri a zamanta na yau Laraba.Lauyan ya roƙi kotun da…

Katsina City News July 16, 2026  ·  12:00 AM
| 124 Views
El-Rufai ya Nemi Afuwar Kotu Bayan ya Janye Wasu Bukatu Uku
El-Rufai ya Nemi Afuwar Kotu Bayan ya Janye Wasu Bukatu Uku


Lauyan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wato Barista Paul Erokoro (SAN), ya bai wa Babbar Kotun Jihar Kaduna haƙuri a zamanta na yau Laraba.


Lauyan ya roƙi kotun da ta ba shi izinin janye buƙatu uku da tawagar lauyoyin wanda ake ƙara suka shigar tun da farko, a inda ya shigar da wata sabuwar buƙatar akan shari’ar zargin  cin hanci da rashawa da hukumar ICPC ta shigar da El-Rufai.

A Yayin zaman kotun wadda Mai Shari’a, Darius Khobo, ke jagoranta, lauyan El-Rufai ya amince cewa buƙatun da ke gaban kotun suna da yanayin salo na takaddama.

Yayin da yake ba kotun haƙuri saboda wahalar da aka jefa ta, ya bayyana cewa ba zai iya amincewa da wasu kalamai da aka yi amfani da su a cikin buƙatun da tawagar lauyoyin wanda ake ƙara suka shigar a baya ba.

Erokoro, wanda ya karɓi shari’ar kwanan nan, ya ce ya yi nazarin dukkan buƙatun da aka shigar a baya, amma saboda yadda suke da salon takaddama, ya ga dacewar ya shigar da sabuwar buƙata.

Advertisement

BSIL Security Report

Ya kuma roƙi kotu ta ba shi ƙarin lokaci domin shigar da sabuwar buƙatar, tare da neman izinin janye buƙatu uku da ke gabanta

Da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan zaman kotun, ɗaya daga cikin lauyoyin masu gabatar da ƙara, Ibrahim Muktar, ya bayyana cewa tun daga ranar da aka ɗage shari’ar zuwa yau, an sake shigar da wasu buƙatu biyu kan wannan batu guda, inda ake neman Mai Shari’ar ya janye kansa daga shari’ar.

Muktar ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda sabon lauyan El-Rufai ya sake shigar da wata buƙata, yana mai cewa hakan wata dabara ce ta jan lokaci, harma ya ce a matsayinsu na masu gabatar da ƙara, suna da alhakin tabbatar da an gudanar da shari’ar cikin gaggawa domin adalci ya tabbata.

Ya ce shari’ar ta zo gaban kotu ne a ranar 6 ga watan Yuli domin fara sauraron shaidu, kuma dukkan shaidun sun hallara. Sai dai lauyan wanda ake ƙara ya shigar da wata buƙata tare da wasu jerin buƙatu da nufin kawo cikas ga ci-gaban shari’ar.

A cewarsa, “An riga an shigar da tuhume-tuhumen kuma masu gabatar da ƙara sun shirya tsaf, amma ɓangaren kariya na ci-gaba da shigar da buƙatu iri-iri. Wannan ne ke ɓata lokaci tare da hana a fara shari’ar yadda ya kamata. Da tuni an yi nisa da shari’ar ba don waɗannan buƙatun ba,” in ji lauyan.

A karshe kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa 22 ga watan Yulin shekarar 2026, a sakamakon roƙon da sabon lauyan El-Rufai ya yi na neman ƙarin lokaci domin shigar da sabuwar buƙata.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 9 + 8?