Katsina Times
Mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara kan harkokin ci gaban al’umma, Alhaji Abubakar Tsanni, ya ajiye mukaminsa na mai ba da shawara ga gwamnan.
Jaridar Katsina Times ta samu tabbacin hakan daga majiyoyi a Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina.
A cewar majiyar, Alhaji Abubakar Tsanni ya rubuta takardar ajiye mukaminsa ne a ranar 22 ga watan Satumba, 2026, inda ya bayyana godiyarsa ga Gwamnan Jihar Katsina bisa damar da ya ba shi ta yin aiki a cikin gwamnatinsa.
A cikin takardar, Tsanni ya bayyana cewa zai ci gaba da nuna godiya da girmamawa ga gwamnatin Gwamnan Katsina bisa damar da aka ba shi na yi wa al’umma hidima a cikin gwamnatin.
A halin yanzu, Alhaji Abubakar Tsanni na shugabantar wasu kungiyoyi da dama da ke gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a da neman sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dikko Umar Radda.
Daga cikin kungiyoyin da yake jagoranta akwai A4A – Arewa for Asiwaju, da kuma GMTD.



Comments (0)
No comments yet. Be the first to share your thoughts!