Mai Baiwa Gwamnan Katsina Shawara Kan Ci gaban Al’umma Ya Ajiye Mukaminsa

Katsina TimesMai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara kan harkokin ci gaban al’umma, Alhaji Abubakar Tsanni, ya ajiye mukaminsa na mai ba da shawara ga gwamnan.Jaridar Katsina Times ta samu tabbacin…

Katsina City News September 23, 2026  ·  12:00 AM
| 185 Views
Mai Baiwa Gwamnan Katsina Shawara Kan Ci gaban Al’umma Ya Ajiye Mukaminsa
Mai Baiwa Gwamnan Katsina Shawara Kan Ci gaban Al’umma Ya Ajiye Mukaminsa


Katsina Times

Mai baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara kan harkokin ci gaban al’umma, Alhaji Abubakar Tsanni, ya ajiye mukaminsa na mai ba da shawara ga gwamnan.

Jaridar Katsina Times ta samu tabbacin hakan daga majiyoyi a Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Katsina.

A cewar majiyar, Alhaji Abubakar Tsanni ya rubuta takardar ajiye mukaminsa ne a ranar 22 ga watan Satumba, 2026, inda ya bayyana godiyarsa ga Gwamnan Jihar Katsina bisa damar da ya ba shi ta yin aiki a cikin gwamnatinsa.

Advertisement

NRS Gateway

A cikin takardar, Tsanni ya bayyana cewa zai ci gaba da nuna godiya da girmamawa ga gwamnatin Gwamnan Katsina bisa damar da aka ba shi na yi wa al’umma hidima a cikin gwamnatin.

A halin yanzu, Alhaji Abubakar Tsanni na shugabantar wasu kungiyoyi da dama da ke gudanar da ayyukan wayar da kan jama’a da neman sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Dikko Umar Radda.

Daga cikin kungiyoyin da yake jagoranta akwai A4A – Arewa for Asiwaju, da kuma GMTD.


Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 1 + 9?