Sanata Yakubu Lado Dan Marke: Ɗan Siyasa dan takara mai hatsarin gaske a Zaben 2027

Bincike da Nazarin Jaridun Katsina TimesDaga Mu’azu HassanGwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, PhD, ya taba bayyana cewa babu wasu ’yan adawa da ke da karfin da zai zama…

Katsina City News September 27, 2026  ·  12:00 AM
| 127 Views
Sanata Yakubu Lado Dan Marke: Ɗan Siyasa dan takara  mai hatsarin  gaske a Zaben 2027
Sanata Yakubu Lado Dan Marke: Ɗan Siyasa dan takara mai hatsarin gaske a Zaben 2027

Bincike da Nazarin Jaridun Katsina Times


Daga Mu’azu Hassan


Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, PhD, ya taba bayyana cewa babu wasu ’yan adawa da ke da karfin da zai zama babbar barazana ga jam’iyyar APC a zaben 2027.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taro da Gidauniyar Zawwiyya ta Mustapha Inuwa ta shirya domin murnar komawar Mustapha Inuwa jam’iyyar APC.


A wajen taron, Gwamnan ya gabatar da dogon jawabi, inda ya yi tsokaci kan ’yan adawa da jam’iyyun adawa, tare da karfafa gwiwar magoya bayan jam’iyyarsa.


Sai dai binciken da Jaridun Katsina Times suka gudanar kan yanayin siyasar jihar Katsina ya nuna cewa, duk da kalaman siyasa da ake yi a bainar jama’a, zaben 2027 na iya kasancewa cike da sauye-sauye da kalubale ga dukkanin manyan jam’iyyun siyasar jihar.


Jam’iyyar ADC da kalubalen cikin gida

Bincikenmu ya nuna cewa akwai wasu kalubale da ke fuskantar jam’iyyar ADC, musamman sakamakon rarrabuwar kai, fargabar shari’a da kuma karancin wasu manyan jiga-jigan masu kudi. 


Wannan na iya shafar karfin jam’iyyar wajen fafutukar neman kujerar gwamnan jihar. Sai dai, hakan ba ya nufin cewa jam’iyyar ba za ta iya samun wasu kujerun tarayya da na Majalisar Dokokin Jihar Katsina ba, musamman idan ta samu damar hada kan magoya bayanta da kuma tabbatar da kuri’un da suka samu.


Haka kuma, jam’iyyun NDC da APM na iya taka rawa wajen zaben 2027, musamman idan suka yanke shawarar marawa wani daga cikin ’yan takarar manyan jam’iyyun APC, PDP ko ADC baya.


Yakubu Lado Dan Marke da zaben 2027

A cikin ’yan siyasar da binciken Katsina Times ya mayar da hankali a kansu a wannan lokacin, akwai Sanata Yakubu Lado Dan Marke na jam’iyyar PDP, wanda yake  neman takarar gwamnan jihar Katsina a PDP. 


Wannan ba shi ne karo na farko da Lado ke neman kujerar gwamna ba, domin ya taba tsayawa takarar gwamnan jihar a lokuta daban-daban.


Waye Sanata Yakubu Lado Dan Marke?

Yakubu Lado Dan Marke dan asalin garin Dan Marke ne da ke karamar hukumar Kankara ta Jihar Katsina. Mahaifinsa, Lado Dan Marke, na daga cikin fitattun ’yan siyasar zamanin jamhuriya ta biyu.


Dangane da shekarun haihuwarsa, akwai bayanai daban-daban da ake samu a wasu kafafen yanar gizo. Sai dai binciken Katsina Times ya gano cewa wasu daga cikin wadannan bayanai ba su yi daidai da bayanan da muka samu ba.


Lado ya yi karatun firamare da sakandare. Haka kuma, an taba samun wasu ce-ce-ku-ce game da bayanan karatunsa na gaba da sakandare, kodayake daga baya an samu bayanan da ke nuna cewa ya ci gaba da karatunsa.

Daga kansila zuwa Sanata Yakubu Lado ya fara shiga siyasa ne ta hanyar neman kujerar kansila. Daga nan ya zama shugaban karamar hukumar Kankara, sannan ya zama dan majalisar wakilai ta tarayya.


Advertisement

NRS Gateway

Bincikenmu ya nuna cewa mahaifinsa, Lado Dan Marke, ya taka muhimmiyar rawa wajen bunkasar siyasar Yakubu Lado a farkon tafiyarsa ta siyasa, musamman wajen samar masa da goyon bayan da ya taimaka wajen samun nasara a wasu zabubbuka.


Daga baya ya zama Sanata. Binciken Katsina Times ya gano cewa akwai wani tsarin siyasa da marigayi Umaru Musa Yar’Adua ya bullo da shi a lokacin, wanda ya shafi bai wa Yakubu Lado damar rike kujerar Sanata na wani lokaci kafin a warware wata matsalar siyasa.


Sai dai, bayan da matsalar ba ta warware ba, Lado ya ci gaba da rike kujerar.


Tarihin takarar gwamna Yakubu Lado ya taba neman kujerar gwamnan Katsina a lokuta da dama. Wasu daga cikin wadannan takararraki sun kasance cikin yanayin ce-ce-ku-ce da zarge-zarge na siyasa daga bangarori daban-daban.


Sai dai a wannan karon, bayan kammala zaben 2023, inda Malam Dikko Umar Radda ya samu nasara a kan abokan hamayyarsa, Lado ya mayar da hankali kan sake gina karfin siyasarsa.

Lado da sake gina PDP


Bayan zaben 2023, daya daga cikin abubuwan da Lado ya mayar da hankali a kansu shi ne tabbatar da karfafa ikonsa da tasirinsa a cikin jam’iyyar PDP ta Jihar Katsina, tare da sake tsara tafiyar jam’iyyar bisa tsarin da yake ganin zai taimaka mata wajen samun magoya baya.

Haka kuma, ya kafa gidauniyar tallafawa karatun ’yan makaranta da kuma shirye-shiryen ciyar da al’umma, musamman a lokacin azumin Ramadan.


Wadannan ayyuka, a cewar binciken Katsina Times, sun taimaka wajen kara fadada sunansa da tasirinsa a tsakanin wasu al’ummomi.

Daga shekarar 2025 zuwa 2026, Lado ya kuma kara kokarin jawo wasu ’yan siyasa da suka samu sabani da jam’iyyunsu zuwa PDP. 


A wannan tsari, ya samu nasarar hada wasu ’yan siyasa da suka dade suna da tasiri a jihar, tare da wasu tsofaffin ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya, wadanda suka shiga tawagar siyasarsa.


Alaka da masu adawa da gwamnati

Tabbas..yakubu na magana ta sirri da wasu na cikin gwamnatin APC a jaha da tarayya.majiyoyi daban daban sun tabbatar mana da haka.

Binciken Katsina Times ya kuma gano cewa Yakubu Lado na da alaka da wasu mutane daban-daban da ke nuna rashin amincewa da wasu manufofi ko ayyukan gwamnatin APC a matakin jiha ko tarayya.


Zaben 2027

Binciken Katsina Times ya nuna cewa zaben 2027 a Jihar Katsina na iya kasancewa wani babban gwaji ga dukkanin manyan jam’iyyun siyasar musamman. APC, PDP da ADC. 

Katsina times

@ www.katsinatimes.com 

Facebook page: katsina city news 

Facebook  page.jaridar Taskar labarai

07043777779.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 6 + 1?