Kasafin Kuɗin TETFund Ya Kai Naira Tiriliyan 1.6 a 2026 — Masari

Daga Wakilanmu @ Katsina TimesShugaban Kwamitin Amintattu na Hukumar Asusun Tallafawa Manyan Makarantu ta Ƙasa (TETFund), Alhaji Aminu Bello Masari, CFR, ya bayyana cewa kasafin kuɗin hukumar ya kai naira…

Katsina City News October 16, 2026  ·  12:00 AM
| 34 Views
Kasafin Kuɗin TETFund Ya Kai Naira Tiriliyan 1.6 a 2026 — Masari
Kasafin Kuɗin TETFund Ya Kai Naira Tiriliyan 1.6 a 2026 — Masari


Daga Wakilanmu @ Katsina Times

Shugaban Kwamitin Amintattu na Hukumar Asusun Tallafawa Manyan Makarantu ta Ƙasa (TETFund), Alhaji Aminu Bello Masari, CFR, ya bayyana cewa kasafin kuɗin hukumar ya kai naira tiriliyan ɗaya da biliyan ɗari shida (₦1.6 tiriliyan) a shekarar 2026.


Ya ce wannan adadi ya ninka kusan sau biyar na kuɗin da hukumar ke samu a shekarar 2023.

Masari ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin taron tattaunawa tsakanin hukumar da masu ruwa da tsaki (Town Hall Meeting), wanda TETFund ta shirya a birnin Abuja.


Ya bayyana cewa a wannan shekarar, hukumar ta tallafa wa manyan makarantun gaba da sakandare guda 271 a faɗin ƙasar nan.


Ya ƙara da cewa kowace jami'a ta samu sama da naira biliyan biyu da miliyan ɗari biyar da ashirin da shida (₦2.526 biliyan), yayin da kowace kwalejin fasaha (Polytechnic) ta samu naira biliyan ɗaya da miliyan ɗari takwas da saba'in da ɗaya (₦1.871 biliyan). Shi kuwa ɓangaren kwalejojin koyar da ilimi (Colleges of Education), ya samu naira biliyan biyu da miliyan hamsin da bakwai (₦2.057 biliyan).


Masari ya kuma bayyana cewa TETFund tana tallafa wa cibiyoyin koyon sana'o'i da ƙwarewa (Skills Acquisition Centres) a kwalejojin fasaha guda biyu daga kowace shiyya a ƙasar nan. Ya ce an kashe naira biliyan goma wajen waɗannan cibiyoyi da ke kwalejojin fasaha.


Advertisement

NRS Gateway

Haka kuma, ya ce hukumar ta ware naira biliyan 48 domin tallafa wa jami'o'i 12 wajen kafa cibiyoyin ƙirƙire-ƙirƙire da bunƙasa harkokin kasuwanci (Innovation and Entrepreneurship Centres).


Shugaban kwamitin amintattun ya bayyana cewa hukumar ta kashe sama da naira biliyan shida wajen gudanar da ayyukan binciken ilimi guda 174 a manyan makarantu daban-daban a faɗin ƙasar nan.


Ya ce TETFund ta yi nisa wajen kafa tare da samar da kayan aiki ga manyan dakunan bincike na zamani masu ayyuka da dama (Central Multipurpose Laboratories) guda shida, inda aka samar da ɗaya a kowace shiyya ta ƙasar nan.


Bugu da ƙari, ya bayyana cewa hukumar tana kafa wasu cibiyoyin ƙwarewa guda shida da za su mayar da hankali kan fannonin fasahar mutum-mutumi (Robotics), rubuta manhajoji (Coding), basirar na'ura (Artificial Intelligence), koyon na'ura (Machine Learning) da kuma tsaron yanar gizo (Cybersecurity).


Ya ce idan aka kammala waɗannan cibiyoyi, TETFund za ta kasance tana da irin waɗannan cibiyoyin bincike da ƙwarewa guda 36 a faɗin ƙasar nan.


Masari ya ƙara da cewa ƙaruwar kuɗaɗen shiga da TETFund ta samu a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na nuna jajircewar gwamnati wajen bunƙasa harkokin ilimi da inganta ci gabansa a Najeriya.


A ƙarshe, ya yi kira ga manyan makarantun da hukumar ke tallafawa da su tabbatar da cewa sun kula da gine-gine da sauran kayayyakin more rayuwar da aka samar musu, domin kare su daga lalacewa da kuma tabbatar da cewa sun ci gaba da amfani ga ɗalibai da al'umma na tsawon shekaru masu yawa.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 3 + 7?