WANE NE ALƘALI PETER ODO LIFU, WANDA YA SOKE JAM'IYYAR ADC YA KUMA SOKE TAKARAR ATIKU?

Tarihinsa da wasu shari'un da suka jawo ce-ce-ku-ceMu'azu Hassan @ Katsina TimesAn haife shi a garin Okpoma, da ke ƙaramar hukumar Yala, a jihar Cross River. Ya yi karatun aikin…

Katsina City News November 06, 2026  ·  12:00 AM
| 27 Views
WANE NE ALƘALI PETER ODO LIFU, WANDA YA SOKE JAM'IYYAR ADC YA KUMA SOKE TAKARAR ATIKU?
WANE NE ALƘALI PETER ODO LIFU, WANDA YA SOKE JAM'IYYAR ADC YA KUMA SOKE TAKARAR ATIKU?

Tarihinsa da wasu shari'un da suka jawo ce-ce-ku-ce

Mu'azu Hassan @ Katsina Times

An haife shi a garin Okpoma, da ke ƙaramar hukumar Yala, a jihar Cross River. Ya yi karatun aikin lauya a Jami'ar Jos, da ke jihar Filato. Ya halarci makarantar horas da ƙwararrun lauyoyi a shekarar 1990.


Ya kuma yi digiri na biyu a fannin kimiyyar siyasa, sannan yana da wani digiri na biyu a fannin aikin lauya daga Jami'ar Ibadan.

Kafin ya zama alƙali, ya yi aikin lauya mai zaman kansa, sannan ya koyar da aikin lauya a Jami'ar Ibadan. Daga baya ne ya zama alƙali, inda a yanzu yake aiki a ɗaya daga cikin kotunan tarayya da ke Abuja.


WASU SHARI'UNSA DA SUKA JAWO CE-CE-KU-CE


Shi ne ya yanke hukuncin da ya shafi jam'iyyar Labour Party, wanda ya haifar da rikicin cikin gida da ya raba jam'iyyar, har yanzu kuma ba ta samu daidaito ba.


Shi ne ya yanke hukuncin da ya umurci hukumar zaɓe ta soke rajistar wasu jam'iyyun siyasa, ciki har da ADC.


Shi ne ya riƙa yanke hukunci kan rikicin jam'iyyar PDP, wadda har yanzu ba ta koma daidai ba.

Shi ne ya yanke hukuncin da ya hana hukumar zaɓe bai wa gwamnatin jihar Rivers kundin rajistar masu zaɓe domin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi da shi.


Advertisement

NRS Gateway

Shi ne ya yanke hukuncin da ya tabbatar wa tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, damar tsayawa takara.


YADDA KOTUNAN GABA SUKA YI WATSI DA WASU HUKUNCE-HUKUNCENSA


Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da hukuncinsa kan soke rajistar wasu jam'iyyun siyasa.

A yanzu haka, jam'iyyar ADC tana da ƙorafin da ta shigar a kansa dangane da wasu shari'u.


KATSINA TIMES

Ku biyo mu ta waɗannan kafafen yaɗa labarai:

Yanar gizo: www.katsinatimes.com

Facebook Page: Katsina City News

Facebook Group: Katsina City News

Facebook Page: Jaridar Taskar Labarai

YouTube Channel: Katsina Times

Lambar tuntuba: 07043777779

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 6 + 8?