Muazu Hassan @ katsina times
Jakadan galadiman katsina Ambasada Sani Bako ya ajiye rawanin shi na jakadan galadiman katsina a masarautar Malumfashi.
Ajiye rawanin ya biyo bayan wata wasika da aka rubuta masa daga fadar galadiman katsina ana neman bayani daga wajen sa akan taron da kungiyar su ta shirya akan matsalar tsaro a jahar katsina, taron da akayi a Abuja, Kaduna da katsina wanda a taron katsina wasu matasa suka tarwatsa shi.ana tsakiyar yin shi.
Takardar wadda jaridun katsina times suka samu an rubuta ma jakadan a ranar 29/8/2025. Ana neman yayi bayanin me yasa bai tuntubi fada ba a matsayin shi na wakilinta kafin wasu bayanai su rika fita har da sunan shi.
Ambasada sani bako ya ba masarautar galadiman katsina amsa a ranar 4 ga watan satumba wanda bayan ya kare kansa kamar yadda wasikar da ya rubuta wadda katsina times ta samu daga karshe ya karkare wasikar sa da cewa ya sauka da mukamin jakadan galadiman katsina da masarautar ta bashi.
Hade da wannan labarin ga wasikun guda biyu .