An yaba wa Gwamna Dikko Umar Radda na jihar Katsina bisa ba kananan hukumomin jihar damar cin gashin kansu wanda ke ba su damar gudanar da ayyukan raya kasa don inganta walwala da jin dadin al'umominsu.
Mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin siyasa, Alhaji Ya’u Umar Gwajo-Gwajo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Katsina.
Sanarwar ta bayyana cewa a baya-bayan nan kananan hukumomin sun gudanar da ayyuka daban daban na kawar da zaizayar kasa da gyaran cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko da dakunan shan magani da kuma gyara masallatai da makabartu a yankunansu.
“Kwana-kwanan nan kowace karamar hukuma a jihar nan ta samu jimillar kudi Naira miliyan 350 domin gudanar da wadannan ayyukan waɗanda su suka nemi su gudanar da aiyukan, kuma aka basu dama.
“Alal misali kowace karamar hukuma ta samu Naira miliyan 200 na aiyukan kawar da zaizayar kasa domin kare gonaki da gidaje da filaye daga zaizayewa, musamman a cikin damina.
“Kafin nan kowace karamar hukuma ta amshi Naira miliyon 100 domin gyarawa da fadada kananan asibitoci da dakunan bada magani, muna da mazabu 361 a jihar nan, an gyara asibiti daya da dakin bada magani daya a kowace mazaba.
“Har ila yau bisa bukatar malaman addini daga kananan hukumomin, an ba kananan hukumomin kudi don gyaran makabartu da masallatai da kuma gudanar da addu’o’i na musamman don dorewar zaman lafiya a jihar, akalla kowace karamar hukuma ta samu jimillar kudi Naira miliyan 30 domin gudanar da wadannan ayyukan”.
Alhaji Ya'u Umar Gwajo-Gwajo ya bayyana cewa kananan hukumomin da ke fama da matsalar tsaro sun amince su rika siyan kayan aiki da bada alawus ga 'yan banga da 'yan sa-kai, da sauran tallafi domin magance matsalar tsaro a yankunansu.
“Wadannan kuɗaɗen, ƙananan hukumomin ne suka kashe su da kansu, kuɗinsu ne kuma su ke zartar da shawarar yadda za su kashe su don inganta walwala da jin dadin al'umarsu.
“Mai girma gwamna a kullum yana tabbatar da cewa duk abin da za ayi, ana yinsa ne bisa doron doka, shi ya sa kananan hukumomi ke da damar kashe kudadensu bisa ‘yanci da zabinsu.
"Su ke biyan albashinsu, da alawus alawus, da kudaden tafiyar da harkar gwamnati, sannan kuma suna gudanar da ayyuka a fannin kiwon lafiya da ilimi, da muhalli da noma, da manyan ayyuka da sauran su domin inganta walwalar al'umarsu", inji Alhaji Ya'u Umar Gwajo-Gwajo.