LAIFIN DANFODIYO GA ‘YAN KWANGILA KAFA DAULAR MUSULUNCI DA WARGAZA GUNGUN MUSHIRKAI

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes14092025_000505_Screenshot_20250914-010417.jpg



Nasiru Adamu El-hikaya @blueprint manhaja 

Duk wanda ya tsaya kai da fata don kafa wani abun alheri don amfanin bani-adama za ka taras ya taka kafar miyagun iri da ke amfana da abubuwan da a ka kawar na kazanta da son zuciya. Ga ma misalai a nan cikin Afurka in mun duba Nelson Mandela a Afurka ta kudu da ya taso da yunkurin yakar nuna bambancin launin fata daga turawa an yi wuf a ka jefa shi gidan yari a Robben Island ya zauna shekaru 18 cikin tsawon shekaru 27 amma ya fito daga karshe ya samu nasarar zama shugaban kasar bayan rugujewar mulkin wariya. Muhammad Morsi a Masar ya lashe zabe a turbar dimokradiyya amma don matakan da su ka hada da bude mashigar Rafah don Falasdinawa su sarara a ka kulla makarkashiya cewa gwamnatin sa ta gaza. A ka marawa sojojin da su ka kifar da gwamnatin baya inda shi kuma a ka caje da aikata laifuka tamkar na cin amanar kasa, a na tsakiyar shari’a ya fadi ya mutu. Thomas Sankara soja ne da ya mulki Burkinafaso cikin hazaka amma haka a ka bindige shi har lahira. Ko nan Ghaddafi a Libya da ya dau matakan daga darajar kasar sa da neman kawo cigaban Afurka ta fuskar wayewa, haka a ka cinna fitina a kasar har mutane su ka yi bore karshe a ka yi ma sa mummunan kisan gilla a kan titi. Alhakin hakan ya sa kurwar Libya ta mutu murus kasar ta zama ba gwamnati mai tasiri. Haka Paul Biya ya ci amanar mai gidan sa Ahmadou Ahijo da ya yi sanadiyyar hawan sa mulki inda ko gawar sa ma sai da a ka hana ta dawowa kasar don illar sharrin wanda ka taimaka. Mun samu labarin wani Shehun malami a Najeriya in ya zo kammala rubuta wasika ya kan nemi tsari daga sharrin wanda ya taimaka. Mu koma can shekaru 271 lokacin haihuwar Shehu Danfodiyo Mujaddadi da tasowar sa a matsayin mai neman ilimi har ya zama gawurtaccen malami kuma ya dukufa ga taimakon al’umma wajen tsamo su daga duhun jahilci da lalaci. Yunkurin na sa ne ya kusa sanadiyyar salwantar da ran sa inda daga bisani Allah madaukakin Sarki ya sanyawa da’awar sa albarka har ya kafa gagarumar Daula daga yankunan daidaikun sarakuna masu mulkin mulukiyya da danniya. Waccar tsohuwar gabar ta Daular da ya kafa ta zama gagagrau har yau, ita ce ta dawo da wani launi na cusa kabilanci da shafa ma sa bakin fenti don samun damar wargaza aikin da ya assasa don yakar musulunci da musulmi ko tunzura musulmi su ajiye addinin su a gefe guda su rungumi kabilanci da hakan zai sa su juya takubba a kan junan su shikenan sai a maimaita kwatankwacin abun da ya faru a Rwanda inda wani daga kabilar Hutu ya fara yayata kamfen cewa ‘yan Tutsi kyankyasai ne don haka a yi ta farautar su a na kashe su. Hakan kuwa a ka yi ta kisan kare dangi don munin yanda kabilanci kan cinye tunanin mutane ya maida su tamkar dabbobi don mantawa da cewa dukkan su ‘yan-adam ne kuma ba wanda ya roki Allah mahalicci ya yi wo shi a wata kabila ko a wani launin fata, wannan hukuncin Allah ne madaukakin Sarki mai yin yanda ya so a lokacin da ya so ko ba a so. 

Me fa’ida a zamanin yau wani lalatacce da bai amfanawa kan sa komai ba bare a je ga gidan su ko ma kauyen su amma zai dubi wanda a ka Haifa tun a shekara ta 1754 ya surfa ma sa zagi. Zan maimaita zaiyana masu wannan hayakin kan ba lallai ne ma musulmi ba ne ko ma ‘yan wata sananniyar kabila ba ce, shaidanu ne da talauci da kazanta su ka yi wa katutu don haka su ka karbi wannan kwangilar daga annamimai masu gaba da rashin wargajewar arewacin Najeriya. Babbar wautar ita ce in fitinar nan ta taso za ta iya zama ta fara ko ta kare a kan su.

Na bi da yawa daga shafukan yanar gizo na ‘yan kanzagin annamimai inda na lura mutanen ma matsorata ne don wa imma ba hotunan su a kan shafukan ko sun rufe zauren bayanan su. Wani abun ma sun kirkiro wasu sunaye na karya da ma bagayen yaudara na amfani da AL waye-waye da babu sunayen a kan takardun su na makaranta in ma sun yi karatun, kai ko a katin asibiti ba za ka ga suna amsa sunayen da su ke lakabawa kan su ba. In ba tsoro ba ga kalubale ga gaggan makiran: duk mai ikirarin shi musulmi ne ko dan uwan mu Bahaushen gaskiya ne, ya wallafa takardan shaidar haihuwar sa a yanar gizo. In ba takardar su manna takardar dan kasa ta karamar hukumar da su ka fito mu ga tabbacin cewa sunan na su ne ko ikirarin kabila da tushen su gaskiya ne. Na tabbata akasarin su makaryata ne masu amfani da sunan bogi don cimma muradun aikin kwangilar yakar musulunci a arewacin Najeriya. Ahir.

Laifin Mujaddadi Danfodiyo ga ‘yan kwangila shi ne kafa Daular musulunci da hatta ‘yan mulkin mallaka sun gaza dawo da matsafa da ‘yan bori. Danfodiyo alheri ne. Lokacin da ‘yan mulkin mallaka su ka shigo Daular Sokoto su ka yake ta sun sha mamaki don samun tsarin mulki na shugabancin musulunci daga sama har kasa. Ga karatun addini da ilimi mai zurfi. Dalilin hakan ya sa su ka gudanar da mulki ta bayan fage wato ta hanyar amfani da sarakuna don isar da sako ga jama’a. A yankin kudancin Najeriya ‘yan mulkin mallaka sun jagoranci yankin kai tsaye da kan su don haka su ka samu nasarar cusawa ‘yan yankin al’adun su na tsiraici da daukar Bature a matsayin mafi daraja a duniya. Har gobe burin wasu mutan kudancin Najeriya shi ne shiga turai ko tafiya kasashen turai kamar Andalus wato Spain, Italiya, Faransa, Burtaniya ko tsallakawa can kudancin Amurka irin Burazil da Cuba. Mujaddadi ya kafa tsarin wayewar Islama inda maza da mata ke karatu don fahimtar yanda za su bautawa Allah da gudanar da rayuwa mai tsabta. Har yau bayan shekara 271 da haihuwar Shehu, shekaru 208 da rasuwar sa, dan arewa mai dattaku bai zubar da al’adar sa ba don ko a tsakiyar London za ka gane shi don tsare kimar sa ta hanyar sa sutura mai kare mutunci. Na taba kawo misalin yanda kakannin gwagwarmayar karbo ‘yanci irin Firaminista Sir Abubakar Tafawa Balewa mai muryar zinari da Sir Ahmadu Bello Sardauna uban ‘yan boko kan shiga har gidan sarauniya Elizabeth da rawani a kan su maimakon kafa malafa ko tsefe gashi kamar wasu baubayin bakar fata da ba su amfana da wayewar Islama da Mujaddadi ya jajirce wajen karfafawa ba. Wannan gado na dattaku da ya hana Bature mayar da mata masu saka kamfai ko dan siket ko maka curin gashin doki a kan su don a dole su zama bakaken turawa. Haushin rashin wanke kwakwalwar al’ummar yankin zuwa dabi’un mai jan kunne ya sa ‘yan kwangila na wannan zamani su ka bullo da hanyar canja tarihi da yada kiyaiyar kabilanci don ruguza yankin da ya gagari makiran baya wargazawa. Samun masallatan salloli 5 da na Jumma’a da kan tara dubban mutane kan ba wa makirai haushi da burin su mutane su fi taruwa wajen kallon kwallon kafa ko ma taron shiririta na masu wasa da maciji ko kura. Maimakon taron shirme na borin na uwale, hawa iskar na babule ko tarewa a gidan mai makarai da su magajiya uwar ‘yan gagara, sai a ka ga sai bude tsangaya da makarantun Islamiyya a ke yi. Ga majalisun tafsirin Alkur’ani da tarukan wa’azi da bigiren karawa juna sani ko kaifafa basira cikin littattafan hadisi da fikihu. An kawo zamanin nan inda har jami’o’i na annurin Islama a ke kafawa a kasar arewa. Ga misalin jami’ar Alkalam, Alhikma da Al’istikama sai Assalam da ke kan hanya. Hakika inda cibiyoyin karta da ludo a ke kafawa ko majalisun ‘yan caca da na ‘yan ludu da madigo ba wanda zai karbo irin wannan kwangilar don dama burin shi ne maida mutanen mu ‘yan duniya hayakin taba daga ‘yan ta more sai kawalai da masu neman na Bello Badun don an ci nasarar kashe mu su zuciya. Bijirewa lalaci, wawanci da sakarci da koyarwar makarantar Mujaddadi ta yi a arewacin Najeriya har ma da cikin kasashen makwabta da su ka hada da wasu yankunan kasar Kamaru da wasu biladis sudani, ya sa lallai sai an haddasa fitina da aibanta Shehu ta hanyar nuna haka kawai ya yaki musulmi don karbar mulki. Tarihin Shehu ya faro ne daga malami mai koyarwa inda wadanda ba sa kaunar addinin gaskiya su ka tilasta shi gudun hijira da ma bin sa har inda ya koma don kashe shi kowa ma mai kin jinin sa ya huta. Gaskiyar magana lokacin garuruwa ne ko ‘yan kasashe da ke karkashin sarakuna da kowace masarauta ke son fadada sarautar ta zuwa makwabta amma ba hangen nesan samun babbar Daula daya mai karbar umurni daga gwamnatin tsakiya ta Amirul Muminina. Tabbas inda turawa sun zo sun samu yankin arewa karkashin sarakuna cikin garuruwa masu tsari daban-daban, za su wargaza yankin ne da kawo tsari mai karbar umurni daga ‘yan mulkin mallaka na maida mutane tamkar bayi.

KAMMALAWA

Da wannan na ke kira ga fitattun masana da masu kishin arewacin Najeriya su fito don takawa wadannan tsirarun ‘yan kwangilar birki tun kafin su ribaci matasa da ba su goge a rayuwa ba zuwa shiga wannan kamfen din na rusa kai da kai. A na yi wa makiri kirari cewa wayo gare ka amma ba ka da hankali. Ina ka ga hankali, ka na gidan gilashi amma ka na wasan jifa!.

Follow Us