’Yan Bindiga Sun Sace Masallata 40 a Zamfara Duk da Yarjejeniyar Sulhu

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes15092025_165422_FB_IMG_1757955217701.jpg

KatsinaTimes | Litinin, 15 ga Satumba, 2025

Kasa da kwana guda bayan rahotannin kulla yarjejeniyar sulhu a wasu sassan Arewacin Najeriya, ’yan bindiga dauke da makamai sun sace akalla masu ibada 40 a cikin wani masallaci da ke kauyen Gidan Turbe, karamar hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.

Shaidun gani da ido sun shaida wa wakilan mu cewa maharan sun afkawa masallacin ne da misalin karfe 5:30 na safe a lokacin sallar asubah, inda suka kewaye wajen sannan suka tilasta wa masu ibada su bi su cikin daji. An bayyana cewa daga bisani aka kaisu cikin dazukan da ke kusa da yankin Gohori na karamar hukumar Tsafe.

Al’ummar yankin sun bayyana tsananin fargaba da mamaki, kasancewar lamarin ya faru ne a daidai lokacin da shugabannin gargajiya da wasu kungiyoyin ’yan bindiga a Jihar Katsina da makwabtan jihohi suka sanar da cimma wata yarjejeniyar tsagaita wuta domin rage tashe-tashen hankula.

’Yan bindigar ba su da jagoranci guda. Ana iya yin sulhu da wasu a Katsina, amma wasu na ci gaba da kai hare-hare a Zamfara, Sakkwato, Kebbi da Kaduna,” in ji wani mazaunin yankin cikin wata tattaunawa da manema labarai.

Masana tsaro na ganin wannan hari a matsayin burbushin rashin ingancin yarjejeniyoyin sulhu, domin kuwa har yanzu kungiyoyin ’yan bindiga na da ’yancin kai suna kai hare-hare ba tare da tsangwama ba.

Har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto, hukumomin tsaro a Jihar Zamfara ba su fitar da wata sanarwa ba dangane da lamarin.

Follow Us